Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Farar Hula Da Kananan Hukumomi Ta Ghana Za Ta Gabatar Da Kudurin Canje-Canje Ga Dokar Fansho


kungiyar ma’aikatan farar hula da na kananan hukumomi na Ghana CLOGSAG
kungiyar ma’aikatan farar hula da na kananan hukumomi na Ghana CLOGSAG

Bayan kwashe shekaru su na kwadago, tsoffin ma’aikata su na fuskantar takaici wajen samun fanshonsu akai-akai.

Wannan rashin tabbas da tsoffin ma’aikata ke fuskanta game da fansho ya sa kungiyar ma’aikatan farar hula da na kananan hukumomi na Ghana (CLOGSAG), babbar kungiyar ma’aikatan gwamnati na kasar ta ce za ta gabatar da kuduri a gaban majalisar dokokin kasa da ke kunshe da canje-canjen da za su taimaka musu a dokar fansho mai lamba 766.

Babban sakataren kungiyar farar hula da na kananan hukumomin Ghana (CLOGSAG), Isaac Bampoe Addo ne ya sanar da hakan a wajen bukin kaddamar da kungiyar ‘yan fansho na kasa (PUSPA) a birnin Accra.

Ya ce, kudurin zai bai wa ma’aikata zabin dakatar da bayar da gudunmuwa ga asusun hukumar inshora ta SSNIT bayan sun kammala biyan na watanni 180, kamar yadda dokar fanso mai lamba 766 ta shekarar 2008 ta nuna.

Ofishin SSNIT
Ofishin SSNIT

Isaac Bampoe Addo ya ce, "Muna tsammanin duk wanda ya samu watanni 180 yana da fansho, don haka zabi ne a gare ni, bayan na ba da gudummawar watanni 180, wato kashi 13.5 cikin 100, zan iya amfani da sauran a wani tsarin fansho na daban”. Ya ce, wannan kuduri ne da za su tura gaba don ma’aikata su samu damar ficewa daga tsarin inshorar SSNIT dake kula da fanshon ma’aikata a kasar.

Dokar fansho mai lamba 766 tana dauke ne da tsarin fansho mai hawa uku, da kuma hukumar sa ido a kan yadda za a tafiyar tsarin yadda ya kamata, wato Hukumar Kula da Fansho ta Kasa (NPRA).

Manufar kafa kungiyar ‘yan fansho ta kasa ita ce tallafawa tare da magance bukatun waɗanda suka yi ritaya, bayan hidimar aiki da suka yi. Haka kuma kungiyar za ta dinga tattaunawa da gwamnati don samar da isassun matakai da hanyoyin da wadanda suka yi ritaya za su samu fansho mai inganci kuma cikin sauki. Shin gwamnati za ta so wannan mataki da kungiyar ma’akata ta dauko?

Hamza Adam Attijany, masani a kan harkokin kudi da tattalin arziki ya ce, lallai gwamnati ba za ta so hakan ba, domin ta kan waiwayi inda ake adana kudin fansho domin rance a lokacin da take bukatar kudi. Yace, tsarin inshorar SSNIT dake biyan ‘yan fanshon na bin gwamnati kimanin GHC miliyan uku da har yanzu ba ta biya.

Mataimakin ministan samar da ayyuka da hulda da ‘yan kwadago, Bright Wireko Brobbey, ya yaba da kafa kunigiyar ‘yan fanshon, kuma ya koka da irin halin kuncin da ‘yan fansho ke fuskanta.

Saurari rahoton Idris Abdallah Bako:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00

XS
SM
MD
LG