ACCRA, GHANA - Hukumomin Ghana suna zargin masu canjin kudaden waje ta barauniyar hanya da taimakawa wajen faduwar darajar Sidi, wani lamari da ke mummunan tasiri kan tattalin arzikin kasar.
Matakin dai ya biyo bayan wani shiri na musamman da hukumomi biyun suke gudanar wa akan ‘yan canjin kudi, wadanda aka fi sani da black market.
Shugabar canjin kudi a bankin Ghana, Adjoa Konadu Torto, ta bayyana cewa yanzu ne suka soma wanna atisayin wanda za su yi a duk fadin kasar kuma matakin da ya sa aka gudanar da atisayin, shine yadda Ghana ke kokawa da yadda darajar cidi ke ci gaba da faduwa.
Sauran matakan sun haɗa da aiwatar da bin dokokin hukumar canjin kuɗin ta kasa wajen yin lasisi, kuma dolene mutum sai ya nuna katin zama ‘dan kasa wato Ghana card, da kuma takardun biyan kudin wutan lantarki a duk lokacin da zai yi canjin kudi.
Shugaban saye da sayar da kudi a Ghana ta ce za’a kara wayar da kan jama'a ta kafofin watsa labarai don ilimantar dasu yadda zasu bi dokoki da ka'idojin canjin kudi, domin su kiyaye kansu daga Black market. Sanna kuma za’a ci gaba da gudanar da atisayen a sauran sassan kasar a ‘yan kwanakin nan.
Muryar Amurka ta kai ziyara a daya da daga kasuwannin ‘yan canji, sai dai shagunansu a kulle, mutum daya da bai yadda ya bayyana sunansa ba, ya nuna rashin jin dadinsa akan kame da akayi musu. Ya ce akwai gyara sosai daga babban bankin kasa kafin a kawo karshen black market.
Mallam Imran Ashiru Dekene masanin tattalin arziki a Ghana ya ce ba zaiyu ace bankin Ghana bata san da zaman ana canjin kudi ta haramtacciyar hanya ba, amma kuma ita ke da hurumin tsaftace yadda ake shigowa da dala a kasar.
Bankin ya gargadi jama’a da su daina shiga harkar kasuwanci canjin kudi ba tare da lasisi ba. Sabida babban laifi ne a gaban doka. Kuma ana sa ran za a gurfanar da wadanda aka cefke a kasuwar ‘yan canji daban-daban anan Accra a gaban kotu.
Saurari cikakken rahoto daga Hawawu AbdulKarim: