Koke koken kasashen da suka fi noman coco a duniya na faruwa ne saboda masu sayen cocoa sun rage wasu kudaden ingancin cocoa wato COCOA PREMIUM da suke samar wa manoma.
Shugaban hukumar COCOBOD a Ghana Joseph Boahen Aidoo ya bayyana cewa rashin tabbatar da farashi mai kyau ya sanya manoman cocoa a kasashe biyun cikin matsanancin talauci.
Abinda kasashe biyun wato Ghana da Cote D'voire ke bukatar da a sake dubawa. Mr Aidoo na jawabin ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki bisa harkar cocoa a Accra babban birnin kasar Ghana.
Shugaban ya ce "ya zamo tilas mu sayar wa nahiyar Turai cocoa kan farashin da suka tsaida mana abinda ba zai yi taimako ba. Mun yi imanin cewa Ghana da Cote D'voire ce kasashe biyun da ke da cocoa mai inganci a fadin duniya tun shaikaru aru aru da suka gabata kuma sai ana kimanta ingancin cocoa dinmu ta hanyar samar ma kasashe biyun da wasu karin kudade sakamakon ingancin cocoa dinsu wato wato cocoa quality premium amma akwai damuwa sosai a ga cewa ana rage yawan wadannan kudaden. A yanzu in ana fuskantan karanci cocoa a duniya farashi na kasa kazalika in cocoa ya bunkasa farashin na kasa. Yace ya kamata ayi bincike saboda bisa tsarin kasuwanci a duk lokacin da aka fuskanci karancin kaya to farshinsa na zuwa sama amma na cocoa ba hakan bane."
Mr Boahen na bukatar da kasashen nahiyar Turai su musanyan kokarin da manoma ke yi gurin samar musu da kudaden suka dace maimakon rage farashin cocoa.
Mallam Saeedu Sulaiman Bomba Geiga mai nazari bisa harkar coco ya ce matakin da masu sayen coco ke dauka na rage kudaden da ake samarma manoman cocoa ya kara sanya su cikin halin kuncin rayuwa
Wani rahoton da Bankin Duniya ya fitar, ya yi nuni da cewa fiye da kaso biyu cikin uku na manoman coco a kasashen biyu, na rayuwa ne da dalar Amurka daya da santi 20 a kowace rana.
Saurari cikakken rahoton Hamza Adams cikin sauti: