Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijer: Manoma Da Makiyaya Sun Kafa Gidauniyar Sayen Hannun Jarin Banki


NIGER: Taron Manoma da makiyaya
NIGER: Taron Manoma da makiyaya

A jamhuriyar Nijer kungiyoyin manoma da makiyaya sun kaddamar da wata gidauniya da nufin tattara kudaden  sayen babban hannun jari a bankin bunkasa ayyukan noma, wato BAGRI, bayan da aka fara yayata labarin yiwuwar bankin mallakar gwamnatin kasar zai koma hannun wasu ‘yan kasuwar waje.

La’akari da yadda rashin mallakar wani kaso a hannayen jarin bankin Banque Agricole wato BAGRI ke zama dalilin maida kungiyoyin manoma da makiyaya ‘yan rakiya a harakokin gudanar da wannan banki ya sa wakilai daga sassan Nijer suka hallara a birnin Yamai don kaddamar da gidauniyar da za ta ba su damar tattara kudaden sayen hannun jari kamar yadda shugaban kungiyar Plate forme paysanne Djibo Bagna ya bayyana.

Bankin BAGRI, wanda ainahinsa banki ne na bunkasa ayyukan noma da kiwo, na fuskantar barazanar fadawa hannun wasu ‘yan kasuwar ketare, matakin da kungiyoyin manoma da makiyaya ke ganinsa tamkar wani babban koma bayan da ka iya shafar shirin samar da wadatar abinci a kasa ne.

Gamsuwa da wannan yunkuri ya sa majalisar kula da sha’anin tattalin arziki da jin dadin rayuwar al’ummar Nijer, wato CESOC, ta dauri anniyar shiga gaba don ganin haka ta cimma ruwa, mafari kenan shugaban majalissar Alhaji Mahirou Ligari ya jagoranci bukin kaddamar da wannan gidauniya.

Kungiyoyin sun ayyana shirin zagaya illahirin jihohin Nijer domin wayar da kan manoma da makiyaya mahimmancin gidauniyar da aka kafa da kuma bukatar shigarsu cikin wannan tsari na neman ceto bankin da ainahi gwamnatin kasar ta kafa a shekarar 2010 domin su.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
XS
SM
MD
LG