Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Mutane 3.6M Na Iya Fuskantar Matsalar Karancin Abinci A Ghana


Akalla Mutane 3.6M Na Iya Fuskantar Matsalar Karancin Abinci A Ghana
Akalla Mutane 3.6M Na Iya Fuskantar Matsalar Karancin Abinci A Ghana

Hukumar samar da abinci da aikin noma ta majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewa al’ummar Ghana miliyan uku da dubu dari shidda na iya fuskantar matsalar matsanancin karancin abinci.

KUMASI, GHANA - Abinda ya ninka har so biyu in aka kwatanta da rahoton matsalan karancin abinci a kasar da hukumar ta fitar a shekarar 2009.

Hukumar ta dogara ne da yawaitar hauhawar farashin kayayyaki da rashin sana'a tare da karancin ruwa da tsadar takin zamani domin aikin noma da dai sauransu, kamar yadda rahoton da ta fitar da hadin gwiwar hukumar kididdiga ta kasar Ghana tare da hukumar abinci da kiwon dabbobi ta MOFA suka bayyana.

Matsalan ke tasiri akan farashin kayan abinci ababban kasuwar Kumashi adaidai lokacin da ake tunkarar azumin watan Ramadan.

Masu sayar da kayan hatsi akasuwar sunce “farashin shinkafa da gyada da wake sunyi tashin gwauron zabo”.

Akasarin manoma musamman a birnin Kumashi sun ce karancin ruwan sama a bana tare da tsadan takin zamani yayi sanadiyar rage yawan abinci da suke shukawa domin kaucewa hasara.

Akalla Mutane 3.6M Na Iya Fuskantar Matsalar Karancin Abinci A Ghana
Akalla Mutane 3.6M Na Iya Fuskantar Matsalar Karancin Abinci A Ghana

Mallam Jafar Dankwabia mai nazari bisa harkar noma da kiwon dabbobi a Ghana na ganin fitar da abinci zuwa kasashen da ke makwabtaka da Ghana saboda babu mai lokacin da abinci ya bunkasa tare da barnata abinci na maida hannun agogo baya a kokarin da ake yi na shawo kan matsalar karancin abinci a kasar.

Daya daga cikin manyan jami’an sadarwa na gwamnatin jam’iyyar NPP mai mulki Mallam Muhammad Awal ya bayyana cewa mamayar Ukraine da Rasha ke yi na tasiri sosai bisa matsalar karancin takin zamani amma kuma gwamnati na daukan matakai.

Ya kuma ce gwamnati ta inganta shirin samar wa ko wane kauye madatsan ruwa, abinda ya ce ya bada gudunmawa sosai domin ganin an shawo kan matsalar karancin ruwa ga manoma yayin da masu binciken yanayin sararin samaniya suka yi hasashen cewa Ghana zata fuskanci karanci ruwan sama a bana.

Saurari rahoto cikin sauti daga Hamza Adams:

Akalla Mutane 3.6M Na Iya Fuskantar Matsalar Karancin Abinci A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG