Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TSAYAR DA MAGANA GUDA NA CIKIN ALAMUN SHUGABA NAGARI


Sanata Abubkar Bukola Saraki
Sanata Abubkar Bukola Saraki

‘’Duk inda mutum ya nemi ya zama shugaba in ya zamana baida gaskiya baida amana bai bin kaidojin shi ba zai bi tsarin da aka shirya ba to gaskiya bai dace da shugaban ci ba al’ummar Nigeria gaba daya sun zabi jamiyyar APC wanda ta samu shugaban kasa kuma ta samu rinjaye a majilisun dattijai dana wakilai to kamata yayoi ace duk wani wanda zai fito ya zama shugaba to ya zama dan jamiyyar APC Kuma ya tafi da tsarin APC idan wani ya tashi yayi wani abu sabanin wannan to gaskiyar Magana to yayi abu sabanin abinda ya dace’’.

Sanata Barau Jibrin Kenan dake wakiltar mazabar Kano ta arewa a zauren majilisar dattawar Najeriya kuma na hannun damar Sanata Ahmad Lawal mutumin da ya nemi shugabancin majilisar .Shi kuwa comrade Muhi Magaji wanda yaso APC ta tsayar dashi takarar majilisar Wakilai daga mazabar rimin gadar tofa cewa yayi abinda ya faru a makon jiya a zauren majilisar dokokin Nigeria ya sabawa demokaradiyya.

‘’Inda zaben da akayi na demokaradiyya ce tunda Magana ce akeyi ta shugabannin majilisar dattawa yan majilsar dattawa 49 na PDP suna wurin mu kuma namu wurin mutum 8 ne ko fiye da haka kadan suke wurin saboda haka idan ka dauko ka gani sai kaga wadanda suka fi rinjaye yan PDP ne inkuma zaben bana munafunci bane dama ba shirya shi aka yi ba, to kamata yayi ace su yan PDP sunga sunfi yawa kuma abinda suka yi dai-dai ne, to su tsaida dan PDP yaci zaben tunda raayin damar su ce’’

Wannan dai ya ta sanya Sanata Barau Jibrin bayyana shakkun wucewar kudurori dama bukatun shugaba Muhammadu Buhari cikin sauki a zauren majilisun biyu.

‘’Koda zauran majilisar PDP ce aka dasa wannan ba zai hana mu muzo muyi aikin mu ba, ba zai hana muyi abinda ya dace da al’ummar mu ba, amma tarnaki kan dole ne asamu akan yadda ake son a gudanar da aiki ta yadda za a kwato dukiyar mutane da aka sata a binciko a binciko irin badakalar da aka shirya lokacin jamiyyar PDP da dai sauran su tunda dai yanzu PDP ce ta riga takafa shugabanci ta kafa shugabanci a majilisu guda biyu’’.

Sai dai Comrade Muhi Magaji na mai raayin cewa anfa taka kundin tsarin APC kuma akwai matukar hadari ga masu yin hakan.

‘’Saraki yana amsa APC kuma ya yarda shi dan APC ne daga abinda yayi idan ka dauko kundin tsarin mulkin jamiyya gaba daya korar kansu suka yi da maganganun da suke yi sun nuna basu da jamiyya, sannan idan ka dauko kundin tsarin mulki kasa sashe na 65 karamin sashe na 1 ko na biyu ne zaka ga inda dole sai mutun yana cikin jamiyyasannan zai zama mamba na majilisa dattawa ko ta wakilai, kuma sannan da jamiyya zata tashi ta kore su Saraki ni fahinta ta shine za a iya zuwa a nemi fassarar kotu a wannan kundin tsarin mulki idan ma suka ce ba zasu shiga cikin wata jamiyya ba, jamiyya ta iya ture sun a tabbata zaman su a majilsa ba zai tabbata ba kuma ba zasu iya zama ba.’’

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG