Takaddamar ta fi tsamari musamman akan zaben shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa biyo bayan zaben Bukola Saraki a matsayin shugaban majalisar wanda ya tsabawa muradun gwamnatin jam'iyyar APC.
Gobe Talata ake kyautata zaton za'a yi zaben sauran shugabannin a jamalisun biyu.
Har wayau wasu na gann jam'iyyar APC tana son a zabi wasu da take ganin sun fi dacewa da mukaman. Amma kuma wasu 'yan majalisun suna son a barsu su zabi wadanda suka fi so ba jam'iyya ta yi masu dauki dora ba.
Bayanan bayan fagge sun nuna jam'iyyar na son a zabi Sanata Ahmed Lawal wanda Bukola Saraki ya kayar a matsayin shugaban masu rinjaye kana George Akume ya zama mataimaki.
Sanata Haruna Goje dake kan gaba wajen zaben Sanata Bukola Saraki yace ba zasu amince da sa bakin wasu da lamarin zai juye ya zama tamkar nadi ba. Yace yau a ce babu shirin bangaranci gobe kuma ace akwai. Su basu san abun da ake ciki ba. Yayi misali da zaben mataimakin shugaban kasa wanda Janar Buhari ya tsamo daga kasar yarbawa.
Sanata Haruna Goje yace ita jam'iyyar tana son ta manna Ahmed Lawal da George Akume su zama cikin shugabannin majalisar dattawa. Yace wannan shirin ba zai yiwu ba. Bukola Saraki ya riga ya kayar da Ahmed Lawal. Tambaya nan ita ce ta yaya Ahmed Lawal zai yi aiki da Bukola Saraki?
Yace dimokradiya ake yi. Tunda Allah ya sa Bukola Saraki ya ci sai a bari majalisa ta yi zabe. Idan Lawal din ne ya ci sai a bashi amma ba a yi dauki dora ba daga sama. Yin hakan ba zai kawo cigaba ga gwamnati ko jam'iyya ba ko kuma zaman lafiya.
Yace dauki dora ne ya korosu daga jam'iyyar PDP sai kuma gashi APC tana son yin abun da suka gujewa. Tursasa mutane da dannesu a ce ga shugabanninku ko suna so ko basa so suka sa PDP ta yi asarar 'ya'yanta. To yanzu sun dawo APC ana son a yi masu abun da suka ki a PDP. Sanata Goje yace su ba zasu yadda ba.
Saboda suna fatan shugaban kasa ya yi nasara yace dole zasu jajirce su tabbatar cewa ba'a yi kuskuren da PDP ta yi ba.
Shugaban kungiyar nazari kan lamuran majalisa Awal Musa Rafsanjani yace har dai za'a gyara dimokradiya ya zama wajibi APC ta shawo kan dukan 'yan majalisar wajen daukar mataki. Misali, kamar roke-roke da shugaban kasa zai yi ya nemi majalisa ta yi domin ta tabbatar cewa ta bashi izinin ya cigaba da tafiyar gwamnati. Idan har bai samu ya yi hakan ba to za'a samu tangarda da tafiyar dimokradiya da kuma yadda shugaban kasa yake son ya gudanar da alamuran mulki.
Rafsanjani ya umurci shugaban kasa ya zauna da jam'iyyarsa domin a samu masalaha akan yadda za'a gyara babbar barakar da ta faru garesu.
Cikin neman masalaha shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya ziyarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya shiga tsakani, wato ya zama tamkar dan marina a tsakaninsu da shugaba Buhari.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.