Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shiga Sharo Ba Shanu Ba zai Haifar Wa Majilisar Dokokin Najeriya da Mai Ido Ba Inji Walid Jibrin


PDP
PDP

An tambayi Walid Jibrinabinda zaice game da badakalan dake faruwa a majilisar dokokin Najeriya sai ya amsa da cewa.

‘’To wato abin cewa anan shine mutane su dorawa kansu abinda bai kamata su dora wa kansu ba aikin majilisa aiki ne na musammam aiki ne wanda aka baiwa mutane hakki suzo suyi wannan aiki na Majilisa muma munyi shi saboda haka shiga katsalandan da mutane suke tayi ba dai dai bane.

Wato abin lura shine mutane, su majilisa tana da hakki tana da aikin ta wanda ya kamata tayi jamiyya itama tana da nata hakki da aikin ta wanda yakamata tayi, duka yan majilisa daga party suka fito amma kuma party takan lura da yanayi da yadda abubuwa suke da yadda zamani yake suyi taka tsantsan na abubuwa wadda ba zai bata al’amurra ba.

Alal musali wato anan mu a jamiyyar mu na PDP mu abinda muka ga yakamata idan mutane suka lura da abinda muka yi na hadin kai muna so ne muga mun hada kai na yan majilisa nan wannan ya taba wannan ya taba a hada kai ayi aiki yadda yakamata shi yasa muka fito da wannan hadin kai da wannan jamiyyar domin a can sunkawo musammam a majilisar dattawa wadda suka kawo Senate President Dan jamiyyar APC mu kuma mukakawo mataimakin sa dan PDP.

To menene na damuwa da mutane suke ki har yanzu da irin wannan hadin kai da mu muke ganin zai kawo muna cikakken zaman lafiya yadda abubuwa zasu tafi kar a matsa a cikin wadannan abubuwan muyi ayi maneji muga yadda kasar nan zata tafi yadda zamu mori kasar nan yadda al’amura zasu canza mana yadda za ayi aiki ba tare da wata rigima wadda ake tayi a majilisa a yanzu ni banga anfanin wannan rigimar ba ko kadan’’.

Bello HabeebGaladanchi ne yayi hirar

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG