Bullowar zargin shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, na ci gaba da karbar albashi har bayan da ya sauka daga gwamnan jihar Kwara, ya tayar da batun karbar fansho duk wata ga tsofaffin gwamnoni da a yanzu mafi yawansu ke Majalisar Dattawa.
Mai sharshi kan al’amuran yau da kullun Mohammad Adamu, yace bada irin wannan fansho ya saba hankalin masu zabe da sauran al’ummar jihohi. Inda yace wannan lamari babu tsoran Allah ciki domin gwamna ya sauka daga kan mulki ya baiwa wanda yakeso, shi kuma wanda aka baiwa ya ci gaba da biyan gwamnan wannan kudade.
Ga tsohon gwamnan Kano, Sanata Kabiru Gaya, yace wannan ba zai zama cin tudu biyu ba, matukar Majalisun Dokokin jiha sun amince a bada wannan fansho.
A cewar Barista Kogo Ibrahim, “Babu wani wuri a tsarin mulkin Najeriya, ko wata doka da ta bada damar ko da anini ne bayan ranar da mutum ya sauka daga kan mukami yaci daga asusun gwamnati.” Ya ci gaba da cewa wannan kudi haramunne.
Masu sharshi dai na ganin yawaitar tsoffin gwamnoni a Majalisar Dattawa kan sanya yawan kutsowar muradun kashin kai cikin muhawarar majalisun, da kuma daukar wasu matakan kare kai daga tuhumar da dukkan tsoffin gwamnonin ke fuskanta a kudin hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC.