Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fashin Bakin Masana Kan Yarjajjeniyar Musanyar Takardun Kudi Tsakanin Najeriya Da China


Takardun kudin Najeriya
Takardun kudin Najeriya

Matakin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dauka na farfado da darajar Naira ta wajen cimma yarjajjeniyar musanyar Naira da takardar kudin China na samun yabo amma fa...

Masana na cigaba da yin fashin baki game da yarjajjeniyar da Najeriya da China su ka cimma na musanyar takardun kudadensu kai tsaye, a wani yinkurin Najeriya na farfado da darajar Naira, wadda ta fadi.

Masanin tattalin arziki Dokta Dauda Muhammed na Jami’ar Ado Bayero ta Kano, ya gaya ma wakilinmu a Lagos Babangida Jibrin cewa wannan yarjajjeniyar, wadda ake kira “Currency Swap” a Turance, na nufin cewa za a rinka samun kudin China kai tsaye ba tare da an yi amfani da dala a matsayin ma’aunin darajar Naira ba. Dokta Dauda ya ce sannu a hankali darajar Naira za ta farfado saboda bukatar dala za ta ragu tsakanin ‘yan kasuwan Najeriya. Wani dankasuwa a birnin Lagos mai suna Chika Chikodi ya ce lallai wannan matakin zai taimaka wajen farfado da darajar Naira.

Haka zalika, wani masanin tattalin arziki mai suna Dokta Ahmed Adamu ya gaya ma Ibrahim Ka-Almasih Garba cewa, wannan matakin zai taimaki Naira na wani dan lokaci, to amma ya kamata a kuma dau matakai daga tushe na karfafa Naira saboda nan gaba ma darajar kudin China za ta karu ta yadda takardar kudin China za ta yi tsada kamar yadda ta dala ta yi.

Ga cikakken rahoto daga Babangida da kuma karshen hirarr Ka-Almasih Garba da Dokta Ahmed Adamu:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
Shiga Kai Tsaye
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG