Shugaban majalisar dattawa Dr Abubakar Bukola Saraki ya gabatar da kasafin kudin da suka amince dashi, wato nera tiriliyon shida da biliyan sabain da bakwai da miliyan dari shida da tamanin.
Adadin kudin da majalisun suka rage ya kama biliyan goma sha bakwai da wasu 'yan kai.
Yayinda da yake bayyana amincewar majalisun kan kasafin kudin Dr Saraki ya yiwa bangaren zartaswa gargadi, cewa ya tabbatar ya yi anfani da kudaden yadda ya dace ba tare da kauce hanya ba.
Onarebul Kawu Smaila mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin majalisa yace yana zaton cewa abun da majalisun suka yi zasu samu yadda dashi domin sun samu fahimta ta aiki tare da majalisun.
Wani abun da ya dauki hankalin jama'a shi ne yadda majalisun suka rage kasafin da kashi goma cikin dari.
Sanata Muhammad Danjuma Goje shugaban kwamitin dake kula da kasafin kudi yace dole ne su yi abun da zai yiwu ba abun da ba zai yiwu ba. Yace tunda aka fara mulkin dimokradiya ba'a taba rage kasafin kudi ba saidai a kara da zara shugaban kasa ya gabatar dashi. Da 'yan majalisa karawa suke yi amma a wannan karon sun rage. Dalilin ragewa kuma shi ne wahalolin da ake ciki da kuma faduwar farashen man fetur. Abun da suka yi taimakon shugaban kasa ne suka yi.
A bangaren majalisar wakilai Ahmed Babba Kaita yace kasafin ya sake wa Najeriya lale. Kasafin kudin bana koina mutum yake a kasar ya tabashi. Kasafin ya kuma sauya makomar kasar domin ya sa hankali akan maganar noma da ma'adanai.
Ga karin bayani.