Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan kasuwa da gobara ta haddasa masu hasara a Adamawa sun koka


Gobara a kasuwar Yola
Gobara a kasuwar Yola

Daruruwan 'yan kasuwa suka yi hasara a gobarar da ta auku a kasuwannin Yola da Limangurore da garin Furfore kusan watanni uku da suka gabata.

'Yan kasuwan suna kokawa saboda kawo yanzu babu wani tallafi da suka samu daga gwamnatin jiha ko ta tarayya duk da alkawuran da gwamnatocin suka dauka can baya.

Yayinda suke jawabi a wajen taron rabon tallafi da wani dan majalisa ya bada, shugabannin 'yan kasuwan sun koka da rashin cika alkawuran da aka yi masu. Yanzu wasunsu sun koma maula domin ciyar da iyalansu.

Alhaji Ali Kachalla shugaban 'yan kasuwar Yola yace har yanzu basu bar mika kokon baransu ba. Sai ya kira gwamna da kakakin majalisar dokokin hijar cewa sun mika kokon baransu garesu.

Shi ma a jawabinsa shugaban kungiyar 'yan kasuwan Najeriya da mataimakinsa mai kula da jihohin arewa Alhaji Muhammad Ibrahim Etisi ya wakilta ya bukaci gwamnatocin arewa da su taimakawa 'yan kasuwa musamman a lokacin da suka fada cikin wani bala'i kamar ta gobara.

Shi ma dan majalisa da ya taimaka masu Onarebul Lawal Garba ya bukaci gwamnatoci da manyan kamfanoni su tallafa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG