Yawancin shugabanni masu mulki suna ganin su ne suke da iko kowa kuma suka kira ya yi aiki dasu dole ne ya zama dan amshin shatansu, dalili ke nan da ake samun kurakurai.
Wadanda aka dauko su yi aiki 'yan daukowa ne basu kware da aikinsu ba. Yawancinsu basu shirya fuskantar aikin da aka daukosu su yi ba.
Farfasa Ango Abdullahi wanda yake ganin mataimakan shugaban kasa yawancinsu basu da nagarta ya yaba da yaki da cin hanci da rashawa da shugaba Buhari ke yi amma mutum daya baya zama shi ne gwamnati. Dole ne ya yi aiki da wasu. Mutum daya baya zama gwamnati kuma ya yi nasara. Shugaba ya yi shugabanci amma ya tara mutane da suka san abun da suke yi ya yi aiki dasu.
Yaki da cin hanci da rashawa daidai ne amma ba shi kadai ba ne aikin gwamnati. Aikin gwamnati ya wuce karban kayan da aka sata. Yace shi a ganinsa shugaba Buhari bashi da mataimaka na kwarai da zasu taimakeshi da aikinsa.
Farfasa Abdullahi yace mafita ita ce shugaba ya sa ido kan masu aiki tare dashi. Ya tabbatar ma'aikata ne na kwarai. Sun sanaikin da suke yi kuma masu gaskiya ne.An san shugaban mai gaskiya ne to sai kuma masu goya masa baya cewa su ma irinsa ne. Akwai alama su masu iyawa ne ko kuma masu kokari ne.
Shugaban ya riga ya fada cewa yana samun cikas daga fannin shari'a. Farfasa Abdullahi yace dama akwai sassa manya uku. Akwai fannin shari'a. Akwai fannin majalisa da kuma fannin zartaswa da shi shugaban yake yiwa jagoranta. Yace dole wadannan bangarorin uku su san gwamnati ba zata samu nasara ba sai sun hada kai sun yi aiki tare.
Ga karin bayani.