Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar kwastan ta Najeriya ta hana shigo da shinkafa ta iyakokin kasa


Ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun da hukumar kwastan ke karkashinta
Ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun da hukumar kwastan ke karkashinta

Daga yanzu hukumar kwastan ta Najeriya ba zata bari a shigo da shinkafa kasar da ta iyakokin ksa.

Kwanturolan kwastan mai kula da jihohin Osun da Oyo shi ya sanarda hakan a taron manema labarai inda ya nuna manyan motocin da suka kama shake da buhuhuwan shinkafa.

Kwanturolan yace gwamnati bata hana shigo da shinkafa ba amma dole a shigo da ita da tashishin jiragen ruwa ba ta iyakokin kasa ba. Yace sun lura kasar bata anfana daga shinkafar da ake shigowa da ita ta iyakokin kasa.

Kwanturolan yace sun kwace buhuhuwan shinkafa dari hudu da garkunan man girki dari biyu da sittin. Sun kuma kama wata mota shake da tsoffin tayoyi.

Adadin kudaden duk abubuwan da suka kama sun kai sub dara nera miliyan 19.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:09 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG