Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya zata kaddamar da manufofin da zasu tabbatar kasar ta samu isasshiyar cimaka - Buhari


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Yanzu dai yawancin cimakar da Najeriya take samu daga kasashen waje take sayowa kamar ire-iren su shinkafa da taliya da wake da dai sauransu.

Jiya Talata shugaba Buhari ya fada a Abuja cewa gwamnatinsa zata dukufa kain da nain ta aiwatar da wasu manufofi da zasu taimaka wurin farfado da fannin ayyukan noma da zai sa kasar ta samu isasshen abinci da zata dogara a kai.

Yayinda yake jawabi lokacn da yake karbar sabon jakadan kasar Bulgaria a Najeriya shugaba Buhari yace gwamnatinsa zata kaddamar da manufofin da zasu sa kasar ta daina dogaro da abinci daga kasashen waje domin cigaba da sayo cimaka daga waje ka iya sa kasar cikin hatsari nan gaba.

Shugaban ya yi la'akari da cewa shigo da abinci barkatai daga kasashen waje ya taimaka wurin ragewa kasar kudaden ajiya kuma ya hana 'yan kasar samun ayyukan yi.

Dole ne mu shuka mu kuma sarafa abubuwan da muke ci. Bamu da arzikin da zamu cigaba da shigo da abinci da zamu iya yi da kanmu daga waje, inji Buhari.

Ya cigaba da cewa "wasu 'yan Njeriya masu hangen nesa sun gina ma'aikatun dake sarafa kayan abinci da aka noma a kasar. Sun kirkiro abubuwan da suka habaka ayyukan yi da zasu rage kashe kudade da kuma kare tattalin arzikinmu".

Shugaba Buhari yace "zamu yi duk iyakacin kokarinmu mu karfafa wasu su hada hannu damu a wannan kokarin samar wa kasarmu isasshiyar cimaka"

Shugaban ya kara da cewa gwamnatinsa zata taimakawa manoma su yi anfani da noman zamani tare da yin anfani da fasahar da zata inganta alabarkatun noma.

Baicin jakadan Bulgaria shgaban ya karbi jakadiyar Australia Hajiya Afsatu Olayinka Ebiso-Kabba da sabon jakadan kasar Saliyo da kuma Thordur Aegir Oskarsson sabon jakadan Iceland. Ya gaya masu Nigeriya zata yi maraba da duk wani kokarin karfafa dangantaka da kasashensu musamman a fannin noma da ma'adanai da kasuwanci.

Shugaban ya yiwa jakadun hudu da suka kasance a fadarsa inda suka mika wasikunsu fatan alheri da samun nasara a aikin da ya kawosu Najeriya

XS
SM
MD
LG