La’akari da hatsarin dake tattare da dorawa wata kabila ko addini laifi a duk lokacin da rikici ya barke a Najeriya, mataimakin shugaban Majalisar Addinai ta kasar NIREC tare da shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci ta kasa, wanda kuma shi ne Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar, sun kalubalanci gwamnati a yayin taron majalisar karo na 2 da aka gudanar a Abuja.
An yi wa taron take da “za’a iya kaurace daura laifi ga wata kabila ko addini da siyasa”.
Gwamnan Jihar Filato wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Arewa Barista Simon Bako Lalong, ya fadi cewa ba daidai ba ne a rika nuna wariya ko bambanci ga wata kabila ko addini ko siyasa.
A kasidar da ta gabatar, Hajiya Salamatu Ibrahim, tsohowar shugabar mata Musulmai a Najeriya, kuma sakatariyar tsare-tsare a majalisar kula da harkokin addinai a kasar, ta ja hankalin shugabanin addinai na Musulci da Kirista wajen nausar da mabiyansu kyawawan dabi’un da addinan suka koyar.
A jawabinsa, babban sakataren majalisar ta NIREC Rev. Cornelius Omonokhua ya ce, ‘yan Najeriya na bukatar canja halayensu da dabi’unsu.
Ya kuma jaddada cewa kada su bari kabilanci da addini su zama tushen raba kawuna na al’ummar kasar.
Daga karshe dai majalisar ta bayyana cewa sai shugabannin gargajiya da addinai sun dauki matakan da suka dace za’a samu mafita ga matsalar da Najeriya ke fuskanata, inda ta bukaci kafofin yadda labarai da su zama masu gaskiya a cikin rahoton da suke yadawa, don inganta zaman lafiya mai dorewa.
Saurari rahoto cikin sauti daga Shamsiyya Hamza Ibrahim: