Kungiyoyin sun kuma yi kira ga shugaban kasar Muhammadu Buhari da kar ya bi sahun wasu kasashen duniya wajen nuna goyon baya ga wani bangare, abin da wasu ke cewa na kara ruruta wutar rikicin.
Kiran na zuwa ne a daidai lokacin a ci gaba da kai hare-hare da Isra'ila da Hamas ke yi wa junansu, wadanda suka yi sanadiyyar asarar rayukan fararen hula a bangarorin biyu.
Cikin wata sanarwa da kungiyar kristocin Najeriya ta fitar da ke dauke da sa hanun sakatarenta Daramola Joseph bade, ta yi kira tare jan kunnen gwamnatin Najeriya da kar ta dauki matakin nuna goyon bayan wani bangare a takaddamar.
Karin bayani akan: Allah, Hamas, Palasdinawa, Isra’ila, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
A bangare guda ita ma kungiyar tabbatar da 'yancin Musulmi a Najeriya MURIC ta yi tir da Allah wadai game da harin da Yahudawan Isra’ila suka kai kan Palasdinawa wadda ya zuwa yanzu aka rasa rayukan mutane sama da 200, ta kuma danganta hakan da ayyukan ta’addanci da cin zarafin bil’Adama.
Cikin karkausar suka shugaban kungiyar Farfessa Isaq Akintola, ya bayyana cewa tun somawar wannan rikici an kashe sama da mutun 200 mafi yawa daga cikinsu yara da mata ne marasa karfi kuma Isra’ila bata damu ba.
‘’Mu yan kungiyar MURIC mun yarda da a tattauna a kan teburin sulhu, ba mu yarda da wani tashin hankali ba domin ba ya cikin dabi’unmu, dole ne majalisar dinkin duniyar ta fito ta sa baki kan wannan aika aika da cin zarafi’
Gwamnatin Najeriya dai ta bukaci bangarorin biyu da su dakatar da wannan rikici da ke haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.
A bangaren Isra’ila mutum 12 rokokin Hamas suka kashe, dukkansu fararen hula illa mutum daya, ciki har da yaro dan shekara 5.
Isra'ila ta ce tana daukan matakan ne saboda katse hare-haren roka da Hamas ke cillowa don ta kare rayukan al'umarta.