Hukumar Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya, UNDP, ta ce ta fara wani shiri na hada hannu da gwamnatin tarayyar Najeriya domin koyawa matasa sana'a ta yadda zasu zamo masu dogaro da kai.
Darektan hukumar ta UNDP mai kula da Najeriya, Samuel Bwalya, shine ya bayyana wannan ga masu neman labarai a Maiduguri, lokacin da yake magana kan daukar nauyin wasu matasan Jihar Borno da hukumar ta yi domin koya musu sana'o'i dabam-dabam.
Mr. Bwalya yace za a kwashe shekaru 5 ana gudanar da wannan aiki na horaswa wanda aka tsara da nufin samar da dogaro da kai, da bunkasa kafa kamfanoni da masana'antu a tsakanin matasan ganin yadda a kowace shekara ake yaye dubban dalibai a makarantun sakandare da jami'o'i.
Mr. Bwalya ya kuma ce zasu yi aiki da hukumomi da ma'aikatu da masana'antu domin tabbatar da cewa wadanda suka samu horaswa din nan sun samu ayyukan yi kafin su zamo masu dogaro da kawunansu idan su na bukatar hakan.
Wasu daga cikin matasa su 50 da hukumar zata horas a Jihar Borno sun bayyana farin cikinsu da wannan.
Wani dan gudun hijira daga garin Banki, Dahiru Ahmed Sulaiman, yace sun ji dadin horaswar share fagen da aka yi musu ta mako guda domin kuwa an gina musu harsashin yadda zasu iya dogaro da kai su kafa wata harkar kasuwanci.
Yace mutum ko ba ya sha'awar yin kasuwanci idan ya halarci wannan horaswa zai samu kwarin guiwar yin hakan.
Facebook Forum