ABUJA, NIGERIA - Wannan doka ce da 'yan majalisar suka ba ta muhimmanci da kuma hanzarta amincewa da ita a cikin kwanaki biyu kacal,
Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa Okpeyemi Bamidele ne ya dauki nauyin dokar maido da tsohon taken Najeriyan, wanda 'yan majalisar ke ganin harrufan da aka yi amfani da su a cikin taken suna da ma'ana sosai kuma zai karfafa gwiwar al'umman kasar wajen kaunar juna da hadin kai da kuma kyautata zamantakewa a tsakanin su.
Sanata Rufa'i Hanga yana cikin masu wannan tunanininda ya ce tsohon taken Najeriyar waka ce da za ta kara karfafa kishin kasa a tsakanin 'yan Najeriya wadanda suka rayu cikin wannan zamanin, kuma sun fahimci muhimmiyar rawar da ta taka a tarihin al'ummar mu.
Hanga ya ce taken Najeriya da ake amfani da shi yanzu sojoji ne suka kawo shi kuma bai yi ma'ana kaman tsohon ba shi ya sa Majalisa ta yi gaggawan amincewa da dokar saboda yaran mu na wannan zamani su yi koyi da kalmomin taken domin ya sauya masu tunani.
Sai dai dan Majalisar wakilai Mohammed Shehu Fagge ya yi suka ne kan matakin da aka dauka na maido da tsohon taken kasar inda ya yi tsokaci cewa a karon farko ma, kawo wannan magana na sauya taken kasar ma rashin sanin ciwon kai ne.
Shehu ya ce a wannan hali da 'yan kasa ke ciki na yunwa, fatara da rashi da sauran abubuwa makamantan wannan. Shehu ya ce shugabanin Majalisa ba su yi tunani ba,domin ba shi ne abinda yan kasa ke so ba.
Shehu ya ce kamata yayi a kalli dokoki da za su amfana wa talakan kasa da abubuwa da za su kawo wa rayuwar su sauyi. Shehu ya ce har yanzu Majalisa ba ta kammala aiki kan kasafin kudi shekara 2024 ba, saboda haka yana kira da a fuskanci bukatun al'umma.
Sai dai Sanata Mustapha Habib daga mazabar kudu ta yamma daga jihar Jigawa ya yaba ne da matakin da majalisa ta dauka inda ya ce yana goyon bayan sauya taken kasar, domin wakar da shi ya sani kenan tun yana yaro. Habib ya ce taken yana da ma'ana kuma zai koyar da ksihin kasa da kaunar juna.
Wannan tsohon taken Najeriya dai wata baturiya mai suna Lillian Jean Williams ce ta rubuta shi a lokacin da Najeriya ta samu 'yancin kai a 1960. An daina amfani da ita a shekara 1978 bayan da aka samo wani sabon taken da wani 'dan Najeriya mai suna Ben Odiase ya rubuta. Dokar maido da taken na jiran sa hannun shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:
Dandalin Mu Tattauna