WASHINGTON, D. C. - Sai dai wasu a cikin ‘yan matan an daura musu auren a wani biki na sirri, kamar yadda kakakin majalisar jihar Neja kuma daya daga cikin ‘yan matan suka bayyana a ranar Talata.
Shirye-shiryen daurin auren da aka yi a jihar ta Neja mai rinjayen Musulmi sun fuskanci suka daga ministar harkokin mata Uju Kennedy-Ohanenye da wata kungiyar kare hakkin a yankin da ta kaddamar da koken dakatar da bikin. Masu suka dai na fargabar cewa 'yan matan, wasu daga cikinsu marayu ne, kuma wasu sun kasa a shekarun yin aure.
Tawagar ma'aikatar harkokin mata ta ziyarci Neja a ranakun Alhamis da Juma'a inda ta gana da kakakin majalisar dokokin jihar Abdulmalik Sarkindaji da wasu limaman yankin da wasu daga cikin 'yan matan, kamar yadda kakakin Sarkindaji Auwal Mohammed ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Mohammed ya ce tawagar ta gamsu da cewa ‘yan matan sun haura shekaru 18, wato shekarar aurar da su bisa doka. Kuma ma’aikatar ta yi alkawarin bayar da tallafin karatu ga duk wadanda ke son ci gaba da karatunsu da kuma tallafin kudi ga masu son yin auren.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna