Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Waiwaye Kan Ayyukan Majalisar Dokokin Najeriya Ta Goma Cikin Shekara Guda


Majalisar Dokokin Najeriya
Majalisar Dokokin Najeriya

Majalisar Dokokin ta doshi cika shekara guda tun bayan da aka rantsar da mambobinta yayin da wannan wata na Mayu Gwamnatin Bola Tinubu ke shirin cika shekara guda da karbar mulki.

ABUJA, NIGERIA - A ranan 13 ga watan Yuni na shekara 2023 ne aka kaddamar da Majalisar dokokin Najeriya ta 10, kamar a lokutan baya tun daga kadammar da ita an fara da gwagwarmayar shugabacin majalisar kafin ma kaiwa ga dokokin da suka dauki hankalin ‘yan Najeriya, musamman saboda kalubale na rayuwa.

Farfesa Abubakar Umar Kari masanin kimiyya, siyasa da ke jami’ar Abuja ya yi mana waiwaye da akan ce adon tafiya a kan majalisa ta 10 da saura kwanaki kadan ya rage ta cika shekara daya da kama aiki.

Majalisa sun yi rawar gani domin sun yi dokoki fiye da dubu daya, dokar da ta kafa Hukumar habbaka yankin Arewa ta Yamma, da dokar habbaka yankunan da ke da ma'adinai, sannan an gyara dokokin cin hanci da rashawa, dokar yaki da kwayoyi, da dokar kididdigar kudade, kuma duk suna da tasiri, akwai wasu da shugaban kasa ya riga ya sa hannu, saboda haka idan za a masu adalci, za a ce sun nuna kuzari.

Sai dai idan za a duba abin da za a fi tuna Majalisar da shi, kaman abubuwan bankada da na ce-ce-ku-ce da suka yi ta faruwa tun daga ranar da aka kaddamar da ita ya zuwa yanzu.

Farfesa Abubakar Umar Kari ya yi karin haske inda ya ce batun zarge-zarge na cin hanci da rashawa da cushe a kasafin kudi da aka dade ana yi a wannan karon ya dau sabon salo domin 'dan majalisar ne da kansa ya tona asiri wannan zargi, watau Sanata Abdul Ningi wannan ya sanya an yi chaa a kan lamarin cewa wannan din ma ya yi daidai da tarihin Majalisun tarraiyya a Najeriya, kaman hargowar zaben shugaban Majalisar dattawa da aka yi.

Kuma har yanzu kura ba ta lafa ba, kusan kan su ma a rabe ta ke, ana zaman dan marina. Kari ya ce abinda kuma ya fi jan hankali shi ne cewa Majalisar tayi ta ware wa kan ta makudan kudade wanda ake cewa kaman na fitan hankali, ga misali kaman kari kan kasafin kudi na bana, da zarge zargen chushe wanda Sanata Abdul Ningi yayi har aka dakatar da shi a Majalisar dattawa.

A takaice dai za a ce irin abubuwa da aka saba gani a Majalisun tarraiyya a Najeriya, ba ta canja zani ba.

Kwararru na ganin majalisar ta kasa yiwa kanta wankan tsarki a kan wadanan zarge zarge da ya sa Forfesa Usman Mohammed masanin siyasa da diflomasiyar kasa da kasa kuma malami a Jami'ar KASU da ke Kaduna yin bayani cewa wannan shekara daya ba a ga wani abu da Majalisa suka yi gagarumi da 'yan kasa za su yaba cewa gara da aka yi ba.

Usman ya ce kudade na 'yan kasa suka yi ta yi wa kansu kaso, sun sayi motoci da kudin yan kasa amma babu wani abin a zo a gani da suka tabuka wa yan kasa. Usman ya yi kira da su fito karara su nuna wa shugaban kasa cewa mutane suna cikin ukuba a kasa.

Majalisa ta goma ta yi kokari na sauya yadda aka dade ana kokarin yin dokar da zata baiwa kanana hukumomi yancinsu ba tare da samun nasara ba, inda kafin kaiwa ga yiwa dokar gyara Sanata Kawu Sumaila ya gabatar da kudurin da ya bayyana mani dubrarar da suke son amfani da ita.

Kawu ya ce majalisar kasa za ta yi tattaki zuwa wurin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu domin a jadadda masa cewa lokaci yayi da zai yi yunkuri na dindindin domin ba kananan hukumomin kasa cin gashin kai, kuma Majalisa za ta goyi bayan sa saboda a cimma nasara.

Sai idai wasu 'yan kasa sun bayyana ra'ayoyi mabanbanta kan ayyukan ‘yan Majalisar. Auwal Musa Rafsanjani shugaban kungiyar CISLAC masu yaki da cin hanci da rashawa tare da sa ido a harkokin Majalisar ya ce yawancin ‘yan majalisar sababbi ne da basu da kwarewa, kuma suna tsoron yin magana kar a ce sun yi ba daidai ba.

Ita kuwa Halima Baba Ahmed shugabar kungiyar kula da mata da yara ta ce ita dai Majalisa ta yi kokari ta tabbatar wa kananan hukumomi yancin cin gashin kansu, domin su ne a kusa da al'umma. Halima ta ce abinda zai fi dacewa majalisa ta sa hankali akai kenan.

Kwararru na bayyana cewa akwai sauran aiki a gaban majalisa ta goma duk da cewa tana da shekaru uku a gabanta da zata yi tana kafa dokokin da zasu taimakawa al'umma kaiwa ga romon dimmukurdiya a kasar

Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:

Waiwaye Kan Ayyukan Majalisar Dokokin Najeriya Ta Goma Cikin Shekara Guda.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:47 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG