Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kudirin Neman Dawo Da Tsohon Taken Najeriya Ya Tsallake Karatu Na 2 A Majalisar Dattawa


Zauren Majalisar Dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)
Zauren Majalisar Dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)

Kudirin da daya daga cikin jagororin majalisar, Opeyemi Bamidele, ya gabatar ya samu gagarumin goyan baya daga 'yan majalisar.

Kudirin neman samun damar Najeriya ta koma kan tsohon takenta ya tsallake karatu na 2 a Majalisar Dattawan kasar.

Kudirin da daya daga cikin jagororin majalisar, Opeyemi Bamidele ya gabatar ya samu gagarumin goyan baya daga 'yan majalisar.

An mika kudirin zuwa ga kwamitocin majalisar kan Bangaren Shari'a dana Kare Hakkin Dan Adam da kuma na harkokin shari'a, inda aka bukaci su dawo da rahoto akansa cikin makonni 2.

'Yan majalisar wadanda da alama galibinsu na goyon bayan kudirin, sun kafa hujja da cewar, tsohon taken zai dabbaka hadin kai, zaman lafiya da bunkasar arzikin kasa, sabanin wanda ake amfani dashi a halin yanzu.

Bayan wata ganawar sirrin da aka tafka mahawara akan kudirin, 'yan majalisar sun ce Taken Najeriyar da ake amfani dashi a halin yanzu gwamnatocin mulkin soja ne suka samar da shi ta hanyar irin nasu dokokin, don haka kamata yayi a watsi da shi domin shigar da akidu da muradan tsarin dimokradiyar Najeriya musammam kara jaddada akidar kasa daya al'umma daya.

An maye gurbin tsohon taken daya soma da "nigeria we hail thee" a turance da wanda ya soma da “arise o' compatriots" a shekarar 1978.

A wani labarin kuma, majalisar wakilai ta zartar da kudirin komawa kan tsohon taken na "nigeria we hail thee".

Cikin gaggawa Majalisar Wakilan ta yiwa kudirin karatu na 1 dana 2 dana 3 inda ta zartar da shi cikin 'yan mintuna.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG