Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GHANA:Sama Da Mutane Dubu Sittin Sun Kamu Da HIV/AIDS Cikin Watanni 6


Dakin binciken cutar HIV
Dakin binciken cutar HIV

Rahotannin baya bayannan da hukumomin a Ghana suka fitar na cewa mutani dubu ashirin da uku da dari hudu da casain da biyar ne gwaji ya tabbatar sun kamu da cutar kanjamau ta HIV tsakanin watan janairun bana zuwa Yuni na shekarar 2022.

Yayin zantawarta da muryar Amurka Rafiya Musah shugabar sashen kulada masu fama da cutar a'asibitin Adabraka PolyClinic dake Accra babban binin kasar Ghana tace masu luwadi madigo da mata masu juna biyu, tare da masu sana'ar karuwanci ke kan gaba cikin jerin wadanda suka harbu da cutar abaya bayannan.


Sai dai a nasa bayanin, mai magana da yawun matsugunin masu luwadi da madigo a Ghana wato LGBTQI da dangoginsu Abdul Wadud Muhammad ya nuna rashin gamsuwa da jawabin hukumar inda yake cewa masu luwadi a Ghana suna isa a gwada su amma mafi yawan alumman kasar basu yin hakan.

Gwajin HIV/AIDS
Gwajin HIV/AIDS

Ya kara da cewa, "in aka ce cutar tafi kama masu luwadi da dangoginsu ba gaskiya bane. Abinda ya kamata mu sani shine mu da muke luwadi a Ghana tare da mata masu juna biyu ne ake gwada mu sosai amma in ana so a san masu yawan kamuwa da cuta to kamata yayi da gwamnati ta fadada gwaje gwajenta a lokacin zata gano masu yawan kamuwa da cutar."

Matsugunan Musulmi na daga cikin wuraren da cutar tafi yaduwa a baya bayannan abinda hukumomi ke bukatar da masu aure fiye da daya su rika gwaji kafin su yi aure.

Dangane da haka, Sarkin Addini ajahar Ashanti na Ghana Dawood Akanni ya bukaci da an ga aluma a rika isa ana gwaji musamman wadanda ke da niyan kara mata tare da daukan matakan kariya domin ganin an dakile yaduwar cutar,

Gwamnati dai ta sanar da daukan matakai ciki har da wasu 245,000 masu fama da cutar da suke samun magani amma babban kalubalenta a yanzu shine anfi maida hankali akan cutar Covid 19 da Marburg.

Saurari cikakken rahoton Hamza Adams cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG