Wakilan majalisar dokokin Birtaniya sun bayyana bacin ransu kan sake yayatawa da nanata bayanan wani Bidiyo dake nuna kiyayya ga musulmi, da shugaban Amurka Donald Trump, ya sake yadawa ta shafinsa na Tweeter wanda kotu ta yankewa wata shugabar kungiya mai nuna wariya a Ingila hukunci kan maganganun fusata jama'a.
Wakilan majalisar da dama sun yi kira ga Firayin Minista Theresa, ta soke "ziyarar aiki da aka shirya shugaban na Amurka, zai kai Ingila badi idan Allah Ya kaimu.
"Shi ba aboki ko kawar mu bane," inji dan majalisa karkashin jam'iyyar Labor David Lammy, ya kuma kara da cewa, Burtaniya bata son ziyarar da Trump zai kai kasar.
Cikin masu sukarsa, har da magajin garin Ingila Sadiq Khan, wanda ya ce yana kara tabbata cewa Burtaniya bata goyon bayan ziyarar da Trump, zai kai kasar, kuma da yawa cikin 'yan kasar za su kalli kalaman Trump ta Tweeter, a zaman abunda ya sabawa dangantaka tsakanin Amurka da Birtaniya.
Kakakin Firayin Minista ya ce "ba dai dai bane" Trump ya sake yayata ko nuna wadannan Bidiyo. Yace " Galibin 'yan Burtaniya basu amince da kalaman wariya da batanci daga wannan kungiya ba, wanda ya saba ala'da da mutunci da kauna da Birtaniya ta dogara akai.
Facebook Forum