Ganin yadda wasu ‘yan mata 26 su ka mutu a tekun Bahar Rum aka kuma gaggauta binne su tun kwanaki 21 gabanin ranar da aka tsayar don binne sun, Najeriya, kasar bakar baka mafi tasiri a duniya, wadda kuma wasu daga cikin mamatan ‘ya’yanta ne, ta bukaci lallai a mata bayanin wannan al’amarin.
Josiah Emeron, kakakin hukumar yaki da safarar mutane ta Najeriya (NAPTIP), ya ce dalilan Najeriya na neman dalili daga Italiya ne saboda ita ce kasar da aka kai gawarwakin mamatan a karshe don haka nauyi ya rataya a wuyansu na yin cikakken bincike.
Da aka tambayi Mai taimaka ma Shugaban Najeriya na musamman kan harkokin kasashen waje, Madam Ikike Dabrie ko me ya sa Najeriya ke ta yin gaba wajen neman kadi bayan kuwa ‘yan Najeriya kadan ne kawai cikin ‘yan matan da su ka mutu din, sai ta ce ai Najeriya kamar uwa ce ga Afirka baki daya. Don haka dukkannin mamatan tamkar ‘yan Najeriya ne.
Ga wakilinmu Hassan Maina Kaina da cikaken rahoton:
Facebook Forum