Ana sa ran wakilan gwamnatin kasar Siriya zasu je Geneva yau Laraba inda zasu yi ganawar neman samar da zaman lafiya wadda Majalisar Dinkin Duniya zata jagoranta, da zummar kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru 7 ana yi.
An fara ganawar jiya Talata inda jakada na musamman na Majalisar Dinkin Duniya Staffan De Mistura ya gana da wakilai daga bangaren ‘yan adawa. Staffan ya ce daga baya bangarorin biyu za su sami damar tattaunawa ido-da-ido a Geneva.
Kamfanin dillancin labaran SANA, mallakar gwamnatin Siriya ya ce jinkirin da aka samu daga bangaren wakilan gwamnati, an same shi ne saboda bukatar da ‘yan adawa suka gabatar akan cewa shugaba Bashar al-Assad ya sauka daga kan mulki a matsayin wani bangaren kafa gwamnatin hadin guiwa.
Wannan batu ya jima yana kawo cikas a shekarun da Majalisar Dinkin Duniya ta shafe tana kokarin shawo kan gwamnatin Siriya da ‘yan tawaye da su yarda da shirin sulhu domin samar da zaman lafiya a kasar.
Facebook Forum