Kur’un da ‘yan majalisar suka jefa a dukkan majalisun tarayyan guda biyu masu yawan gaske ne, kuma dukkansu bai daya ne. Kuma wannan shine karo na farko da majalisun kasar suka yi jifa da duk wani shirin doka da shugaba Obama ya sa wa hannu.
Wakilai 97 suka jefa kurik’ar amincewa da kawarda matsayin na Obama a a majalisar dattawa sun kada kuru’u 97, yayinda mutum daya ne kacal, Harry reid, wanda kuma shine madugun marasa rinjaye na majalisar, ya jefa kuri’ar dake goyon bayan Obama.
A majalisar wakilai kuwa wadanda basu ra’ayin shugaban sune suka samu rinjayi da kuru’u 348 a kan kuru’u 77 na masu goyon bayan shugaba Obama.
Wannan mataki na majalisun kasar yana zama babban nasara ga iyalan wadanda suka mutu a harin ta’addanci na 11 ga Satumban 2001.
Izuwa yanzu kokarin da suke yin a gani an yi musu adalci a nan Amurka na samun tarnaki sakamakon dokar rigakafi dake kare Saudiya.
Shugaba Obama ya shaidawa gidan telbijin CNN cewa wannan mataki na majalisa na baiwa mutane damar su kai karar hukumomin na Sadiyya kotu a kan wannan batu, kuskure ne.