Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hillary Clinton da Donald Trump Sun Koma Fafutikar Neman Zabe


Dan Republican Trump da 'yar Democrat Clinton
Dan Republican Trump da 'yar Democrat Clinton

Yayin da saura makonni 6 kawai suka rage kafin zaben shugaban kasa a nan Amurka, masu kwadayin hawa kan wannan kujera Hillary Clinton da Donald Trump sun koma bakin yakin neman zabe jiya Talata, inda suka caccaki juna bisaga irin rawar da suka taka a lokacin muhawararsu ta farko da aka nuna a telebijin.

Wasu kwararu masu zaman kansu da yawa sun nuna cewa Clinton ce ta lashe wannan mukabala ta daren litinin, kuma ta yiwu ta kara ba ma Trump rata a kuri’un neman ra’ayoyin jama’a da suka nuna cewa tana gabansa da kadan a yanzu.

A lokacin da ta ke wa magoya bayanta jawabi, Clinton ta ce abokin takararta bai bada cikakken bayani ba a lokacin muhawarar.

Clinton ta ce “na sami damar fadin abubuwa kadan da zan yi in na sami nasarar zama shugabar kasa. Kuma kun san ina da wannan dabi’ar ta, in na ce ku zabe ni, to ya kamata in fada muku me zanyi muku.

Shi kuma Trump a lokacin wani gangami jiya Talata a jihar Florida, bayan muhawarar da ya ce yayi nasara, ya nuna cewa zai iya yin abinda ya fi haka.

“Tsawon minit 90, na nazarce ta sosai amma kawai dai na kame kaina. Don bana so inyi wani abun da zan kunyata ta, inji Trump.

Yan takarar biyu zasu kara yin muhawara har sau biyu kafin ranar 8 ga watan Nuwamba, muhawarar da za a kara yi nan gaba ita ce ta ranar 9 ga watan Oktoba in Allah ya kaimu.

XS
SM
MD
LG