Barnar da hare-haren suka yi ta sa an dakatar da yin aiki na dan lokaci a asibitocin, abinda ya kara kawo tsaiko wajen jinyar marasa lafia a birnin da ya fuskanci hare-hare mafiya muni a cikin shekaru fiye da 5 da aka yi ana fada akasar.
Asibitocin M2 da M10 na wani bangaren Aleppo dake hannun ‘yan tawayen dake adawa da shugaba Bashaer al-Assad.
A makon nan ne dakarun Siriyya suka sanar da kai wani sabon farmaki don kwace ikon birnin. Wannan matakin ya biyo bayan rugujewar yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma ta baya-bayan nan a kasar da niyyar kai agajin abinci da magunguna a Aleppo da wasu wuraren. Kayayyakin kadan aka iya kaiwa, kuma hari ta sama ya shafi wata tawaga da ta je Aleppo din.
Adham Sahloul na kungiyar likitoci ‘yan asalin Syria dake Amurka, ya fada yau Laraba cewa da gangan ake kai hare-haren, kuma likitocin 29 kawai aka bari a gabashin Aleppo don su kula da mutane dubu dari uku da hamsin.