Sakamakon binciken da aka fitar jiya Laraba ya tabattar da gaskiyar makamancin wannan binciken da wata Hukuma ta kasar Holland ta gudanar da ya cimmamatsayar cewa jirgin Malaysia kirar MH17 da ya fadin makami da Rasha ta aika ne ya kakkaboshi, zargin da ita Rashan ta musunta.
Rahottanin sun nuna cewa ‘yan tawaye masu ra’ayin Rasha ne suka nemi a kawo musu wannan makamin izuwa kauyen Pervomaysk, kuma lokacinda ya iaso, sun sanar cewa ya iso a gabashin kasar ta Ukraine.
Rasha dai tayi watsi da sakamakon bincike da hukumomin binciken na Holland suka yi.