Peres, wanda ya fuskanci kasawar jikinsa kamar makkoni biyu da suka wuce, ya rasu ne yau Laraba a wata assibiti dake HaShomer.
Kusan duk wani babban mukmamin siyasa da ake rikawa a kasar tashi – ka ma daga Frayim minister, ministan tsaro, ministan harakokin waje da shugaban kasa – duk Peres ya rika su.
Haka kuma a duk tarihin Isra’ila shine yafi kowa dadewa yana zaman Dan-majalisar Dokokin kasar, mukamin da ya rike na tsawon shekaru 48.
Kuma, abin mamaki, Peres ba ma dan kasar Isra’ila na asali bane, a kasar Belarus aka haife shi, ya koma Isra’ila ne da zama yana yaro dan shekaru 11 kacal da haihuwa, lokacin ma Isra’ila na karkashin mulkin mallakar Birtaniya.