A ranar Assabar daruruwan tsoffin sojojin Syria ne suka gabatar da kan su ga sabbin shugabannin kasar, a karon farko tun bayan hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad, domin amsa tambayoyi kan ko suna da hannu wajen aikata laifukan cin zarafin fararen hula, domin yi musu musanyar da afuwa da komawa cikin rayuwar farar hula.
Tsoffin sojojin sun yi tururuwa zuwa wani babban ofishin jam'iyyar Assad ta Baath a Damascus, wadda ta yi mulkin Syria tsawon shekaru sittin.
Matambaya daga cikin tsoffin ‘yan tada kayar bayan da suka sami kwace iko da Damascus a ranar 8 ga watan Disamba, sun gana da tsoffin sojojin tare da ba su jerin tambayoyi da lambar rajista. An kuma ba su damar su tafi abinsu.
Wasu daga cikin dakarun rusasshiyar rundunar soji da jami'an tsaro da ke jira a wajen ginin, sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press cewa, sun shiga cikin sojojin Assad ne saboda samun kudin shiga na wata-wata, da kuma shirin kula da lafiya kyauta.
Faduwar gwamnatin Assad ta zo wa mutane da dama da mamaki, a yayin da dubun-dubatar sojoji da jami'an tsaron sa suka kasa dakile 'yan tada kayar baya.
Yanzu da ‘yan tawayen suka kwace mulkin kasar, kuma Assad yana gudun hijira a Rasha, sabbin hukumomi suna gudanar da bincike kan ta'asar da sojojin Assad suka aikata, da manyan kaburbura da jerin gidajen yarin da sojoji da hukumomin leken asiri da na tsaro suka yi kaurin suna na amfani da su, wajen azabtar da jama’a, da kisan gilla da kuntatawa.
Dandalin Mu Tattauna