Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Martanin 'Yan Siriya Mazauna Turai Kan Hambarar Da Gwamnatin Bashar al-Assad


Syria 8 ga watan Disamba, 2024.
Syria 8 ga watan Disamba, 2024.

Shekaru fiye da goma kenan da Syria ta fada cikin rikicin yakin da ya daidaita kasar tare da tilasta wa miliyoyi rikidewa zuwa yan gudun hijira, sai dai an wayi garin ranar Lahadi da labarin hambarar da Bashar al-Assad da ya shafe kusan shekaru 25 yana mulkin kasar.

Wasu daga cikin ‘yan kasar da suka nemi mafaka a sassan Turai sun bayyana shakku a game da komawa kasarsu ta asali a yayin da masana ke bayyana fargaba kan makomar kasar.

Sa’o’i kalilan da sanarwar 'yan tawayen Siriya ta nasarar kwace iko da kuma hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad, wasu 'yan Siriyan da suka nemi mafaka a kasashen Turai suka soma mayar da martani kan al’amarin na ba-za-ta.

Audrey Mansur na daya daga cikin 'yan kasar Siriya miliyan daya da suka sami mafaka a Jamus a karkashin gwamnatin Angela Merkel na wancan lokacin, ta ce duk da tana cike da farin ciki amma zai yi wuya ta kama hanyar komawa Siriya a yanzu.

Ayoub Tarif da shi ma ke gudun hijira a Jamus ya ce, abin farin ciki ne a rayuwarsa da ya ga an kawo karshen mulkin Assad, da ya kira na danniya, sai dai duk da haka yana dari-dari da salon mika wuya da ya yi.

Shi kuwa Ahmed Abdourahman ya na daga cikin 'yan Siriyan da suka jima suna fafutukar ganin kasar ta kubuta daga abin da ya ce, mulkin kama karya ne.

Yayin da wasu ciki har da manyan shugabanin wasu kasashen duniya ke maraba da faduwar dadaddiyar gwamnatin ta Assad, wasu kuwa na nazari kan irin darasin da ya kamata a dauka daga al’amarin na Siriya.

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa hambararren shugaban da iyalansa sun samu mafakar siyasa a kasar Rasha.

Bashar al-Assad mai shekaru 59 da haihuwa dai, an rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Siriya jim kadan bayan mutuwar mahaifinsa a shekarar 2000.

A lokacin mulkinsa ne kasar ta fada cikin kazamin yakin da ya janyo asarar dubban rayuka, baya ga tilasta wa miliyoyi barin kasar da jefa sauran 'yan kasa cikin wani yanayi na bukatar taimako.

Saurari cikakken rahoto daga Ramatu Garba Baba:

Syria Bayan Shugaba Assad
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG