Ministocin wajen kasashen Turai (EU) na dab da tattaunawa a kan yadda za'a sassautawa Syria takunkuman a yayin taron da zai gudana a birnin Brussels a ranar 27 ga watan Janairun da muke ciki.
Shugabannin kasashen Turai sun fara sake nazarin manufofinsu a kan Syria tun bayan da kungiyoyin 'yan tawaye suka hambarar da Shugaba Bashar Al-Assad, karkashin jagorancin kungiyar HTS, wacce Amurka da kasashe da dama har da Majalisar Dinkin Duniya suka ayyana a matsayin ta 'yan ta'adda.
Takardar da kasashen Jamus, Faransa, Netherlands, Sifaniya, Finland da Denmark suka rattabawa hannu, ta ce ya kamata kungiyar EU ta gaggauta fara sassauta takunkuman da suka kakaba a kan Syria".
Duk da haka, takardar ta kuma yi gargadin cewa, matukar aka gaza cika mafi karancin mizanin mutunta hakkokin bil adama dana 'yan tsiraru, ba za a ci gaba da janye raguwar takunkuman ba kuma nan take za a sake mayar da wadanda aka janye
A makon da ya gabata Amurka ta fitar da yarjejeniyar janye takunkumin hulda da hukumomin gwamnatin Syria tsawon wata 6 a wani yunkuri na sassauta gudanarwar tallafin agaji.
Dandalin Mu Tattauna