Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar PDP ta Bar Mutane Inji Atiku Abubakar


Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya
Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya

A karo na biyu tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubaka ya sake ficewa daga jam'iyyar PDP

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya ya sake ficewa daga jam'iyyar PDP ya shiga jam'iyyar APC. To ko menene dalilin yin hakan a wannan karon?

Wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda ta samu ta zanta da Alhaji Abubakar kan dalilan da suka sa ya bar jam'iyyar da yana cikin wadanda suka kafata. Duk da wai ya taba cewa jam'iyyar PDP gidaje ce gareshi domin haka ba zai fita daga gidansa ba sai gashi yanzu ya ce ya fita domin wai duk manufofin kafa jam'iyyar babu daya da ake anfani da su yanzu. Ya ce an kafa kwamiti na Alex Ekueme an sake kafa na Janaral Nwachukwu domin a samu a yi gyara amma an ki bi. A halin yanzu ita jam'iyyar PDP ta bar mutane, ta bar magoya bayanta, ta kuma bar 'yan Najeriya.

Dangane da ko menene ya sa bai ba sabon shugaban jam'iyyar dama ba ya ga ko zai iya yin gyara sai ya ce an taba yin haka da can amma ba.a yi gyaran ba. Shuganaci na uku ke nan ake kai a kokarin yin gyara amma an kasa yin komi.

Inji Atiku Abubakar matsalar jam'iyyar shi ne rashin samun banbanci tsakanin mulkin jam'iyyar da mulkin kasa. Amma an dauki mulkin jam'iyya da na kasa an dunkulawa hanu daya. Ba'a yi mulkin kasa yadda ya kamata ba kuma ba'a yi mulkin jam'iyya yadda ya kamata ba. Wanda ya ke gwamnati ya kamata ya fuskanci aikin gwamnati ne. Ya kula da yadda kasa zata cigaba da zaman lafiya da tattalin arziki da dai sauransu. Wanda ya ke shugabancin jam'iyya kuma a bar mashi aikin jam'iyya. Kada ya shiga harkar gudanar da ayyukan gwamnati.

Kowane tabbaci ne Atiku Abubakar ke dashi cewa jam'iyyar da zai koma ba zata zama kamar PDP ba sai ya ce jam'iyya sabuwa ce domin haka akwai dama na kafa sabon tubali. Ya kara da cewa ya shiga jam'iyyar APC ne domin ya rayata yadda jama'ar Najeriya zata anfana. Yanzu ba batun takara ake yi ba. Yana son a gina jam'yyar da zata karfafa dimokradiya da cigaban kasa.

Ga cikakken rahoron firar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:50 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG