Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Masu Basira Abdulmalik Mai Buredi

Wani mai tallar kaya a mahadar hanya da ake kira Life Junction, a Abuja, babban birnin Najeriya. Matasa da yawa sun dogara ne kan irin wadannan kananan ayyuka don samun abin sanyawa a bakin salati saboda rashin ayyukan yi a kasar

Cikin shirin matasa masu basira mun sami jin tarihin Abdulmalik Saidu Mai buredi dalibi ne wanda ya dogara da sana’ar saida buredi yan biyawa kan shi bukatu, kuma yayi almajiranci a baya.

An dai haifi matashin ne a garin Gusau, haka kuma tun yana yaro iyayensa suka tura shi almajiranci wani gari da ake kira ‘dan sadau. Alokacin ya da shekaru 6 zuwa 7, ya koma gida daga almajiranci yana da shekaru 12 a duniya, inda aka saka shi a makarantar firamare tare da koya masa yin sana’ar saida buredi.

Yanzu haka dai Abdulmalik ya kammala firamare da sakandare harma yana karatun a kwalejin horas da malamai, wanda kuma har yanzu yana wannan sana’a ta shi ta saida buredi.

Domin sauraren cikakken tarihin Abdulmalik danna nan.

XS
SM
MD
LG