Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Legas Ta Dakatar Da Aikin Jigilar Kiristoci Masu Zuwa Isra’ila Ibada


Jami'an hukumar kula da jin dadin Kiristoci masu zuwa ibada kasar Isra'aila ta jihar Legas da na kasar Isra'ila (Hoto: Facebook /CPWB)
Jami'an hukumar kula da jin dadin Kiristoci masu zuwa ibada kasar Isra'aila ta jihar Legas da na kasar Isra'ila (Hoto: Facebook /CPWB)

“Hukumar za ta sanar da sabon lokacin da za a ci gaba da jigilar masu zuwa ibada a zango na biyu.” Sanarwar hukumar ta ce.

Jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya ta dakatar da jigilar Kiristoci masu niyyar zuwa Isra’ila ibada bayan barkewar yaki tsakanin Isra’ilar da Falasdinu.

A ranar Talata 10 ga watan Oktoba rukunin masu ibada na biyu ke shirin tashi zuwa kasar ta Isra’il domin yin ibada, amma hukumomin jihar suka sanar da soke tafiyar.

Sakatariyar Hukumar da ke kula da jin dadin Kiristoci masu niyyar zuwa ibada a Isra’ila, Mrs. Florence Gbafe, ce ta sanar da wannan mataki cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafin Facebook.

“Hukumar za ta sanar da sabon lokacin da za a ci gaba da jigilar masu zuwa ibada a zango na biyu.” Sanarwar ta ce.

A cewar Mrs. Gbafe, tun a ranar 8 ga watan Oktoba rukunin farko ya kammala ziyarar ibada a kasar ta Isra’ila, kuma tuni ya komo Najeriya.

A ranar Asabar sabon yaki ya barke tsakanin Isra’ila da Hamas da ke yankin Gaza bayan da mayakan Hamas suka kutsa kai kudancin Isra’ila tare da cilla dubban rokoki da suka halaka sama da mutum 700.

Hakan ya sa Isra’ila ta kai hare-haren ramuwar gayya, inda ta kashe sama da mutum 600 a cewar sabbin alkaluman da aka fitar a ranar Litinin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG