Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Bukaci China Da Ta Nuna Mata Goyon Baya, Bayan Da China Ta Ki Yin Allah Wadai Da Hare-Haren Hamas


China Israel
China Israel

Ma'aikatar harkokin wajen kasar China a jiya Lahadi ta mayar da martani kan harin ba-zata da mayakan Hamas suka kai kan Isra'ila, inda ta yi kira ga dukkan bangarorin da su yi taka-tsantsan, kamar yadda Rasha ta bayyana.

"Kasar China ta damu matuka kan yadda tashe-tashen hankula ke ta karuwa a tsakanin Falasdinu da Isra'ila. "Muna kira ga bangarorin da abin ya shafa da su kwantar da hankula, su kuma kawo karshen tashin hankalin nan take, don kare fararen hula, da kaucewa tabarbarewar lamarin,” in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar China.

Kakakin ya kara da cewa, "Hanyar magance wannan rikicin ta ta'allaka ne kan aiwatar da yarjejeniyar kasashen biyu da kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta."

Harin Hamas a Isra'ila
Harin Hamas a Isra'ila

Wani jami'in ofishin jakadancin Isra'ila a birnin Beijing a jiya Lahadi ya rubuta a dandalin sada zumunta na X cewa, Isra'ila ta sa ran China za ta yi Allah wadai da Hamas da kakkausar murya.

Yuval Waks, wani babban jami'i a ofishin jakadancin Isra'ila da ke birnin Beijing ya shaida wa manema labarai jiya Lahadi cewa, "Lokacin da ake kashe mutane ana yankasu a kan tituna, wannan ba lokaci ba ne da za a yi kira da a samar da maslaha tsakanin kasashen biyu ba ne."

Ita dai China ba ta sanya kungiyar Hamas da ke Gaza a matsayin kungiyar ta'addanci ba amma tana kallonta a matsayin kungiyar gwagwarmaya.

Ofishin jakadancin Isra'ila a China ya kuma bukaci China da ta goyi bayan Isra'ila.

"Muna fatan kasar China za ta iya ba da hadin kai da goyon baya ga Isra'ila a wannan mawuyacin lokaci," kamar yadda ta rubuta a dandalin sada zumunta na X.

Dangantakar tattalin arziki tsakanin China da Isra'ila ta kara habaka cikin shekaru 30 da suka gabata tun bayan kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu a shekarar 1992, ko da yake ana ci gaba da samun sabani na siyasa. Wadannan sun hada da rarrabuwar kawuna kan batutuwan da suka shafi Falasdinu, dangantakar kasar China da abokan adawar Isra'ila, irinsu Iran, da damuwar da Isra'ila ke da ita kan harkokin tsaro dangane da fasahohin da ta ke yi wa kasar China.

"Kasar China tana da alaka mai karfi da Isra'ila, amma ta dogara ne kan aniyar Isra'ila nasamar da fasahar zamani, gami da fasahar soja ga kasar China. Dangantakar tattalin arziki tana da karfi, amma China da Isra'ila suna da manyan bambance-bambancen diflomasiyya. Misali, kasar China tana da alaka ta kut-da-kut da Iran. A ko da yaushe kasar China tana goyon bayan kasar Falasdinu wajen samun 'yancin cin gashin kanta, don haka a siyasance tana adawa dayawa da wasu daga cikin manufofin Isra'ila," a cewar Dennis Wilder, mataimakin farfesa a fannin nazarin Asiya a jami'ar Georgetown, ya shaida wa Muryar Amurka ranar Lahadi.

Kasar China ta yi kokarin kulla kyakkyawar alaka da Isra'ila da Falasdinu, don haka da wuya ta goyi bayan bangare guda, a cewar Bonnie Glaser, manajan daraktan shirin Indo-Pacific program at the German Marshall Fund na Amurka.

Glaser ya shaidawa Muryar Amurka cewa, "Kamar mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, China za ta kauce wa zargin wani bangare, amma a maimakon haka za ta yi kira da a kawo karshen tashin hankalin."

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG