A Nijar kungiyoyin farar hula da kungiyoyin gwagwarmaya sun kammala muhawara tare da mayar da martani kan matakin kungiyar Tarayyar Afirka na amincewa da juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar, da ma gabatar da jaddawalin taimaka wa hukumomin mulkin sojan kasar kan komawa tafarkin tsarin mulki.
Bayan wani zama da kwamitin sulhun kungiyar Tarayyar Afrika tayi kan batun rikicin siyasar Nijar ne kungiyar ta bayyana amincewarta da juyin mulkin Nijar, tare da nada wakili na musamman daga kungiyar wanda zai sanya ido kan tafiyar mulkin rikon kwarya, har daga karshe a mayar da kasar turbar dimokaradiyya.
Kwamitin ya ja hankalin kungiyar ECOWAS da sojojin da ke mulki a Nijar da su sasanta domin tattaunawar neman hanyoyin warware rikicin siyasar kasar cikin lumana, a saboda haka ne kungiyoyin farar hula suka shirya wata muhawara mai taken samar da hanyoyin magance matsalar siyasar Nijar cikin ruwan sanyi, inda kungiyoyin suka bukaci kungiyar ECOWAS ta bi sahun takwararta ta Afrika kan batun juyin mulkin da aka yi a Nijar.
Traore Hamidu, shugaban gamayyar kungiyoyin farar hula na jihar Agadas, ya ce suna jan hankalin ECOWAS don ganin an warware lamarin cikin ruwan sanyi.
Kungiyar ta Afrika ta sanar da wannan matakin ne a lokacin da kungiyar ECOWAS da hukumomin mulkin sojan Nijar suka kwashe watanni ba tare da an samu wata matsaya ba, yayin da jama'ar Nijar ke ji a jikinsu sakamakon takunkumin karya tattalin arziki da aka sanya wa kasar.
Da yake tsokaci game da batun, Musatafa Alhaji Adam, wanda dan gwagwarmaya ne a Nijar, ya bayyana goyan bayansu ga matakin na Tarayyar Afrika.
A bangare guda kuma hukumomin mulkin sojojin Nijar sun bukaci tattaunawa da ECOWAS domin warware rikicin kasar ta hanyar lalama, wanda tuni masana harkokin yau da kullum irinsu Abdurahamane Dikko suka soma bayyana ra'ayoyi kan matakin sojojin.
Kungiyar Tarayyar Afrika ba ta dai ambaci batun maido da hambararren shugaba Muhammed Bazoum a kan mulki ba, sai dai kawai ta yi kira da a sake shi da iyalinsa da duk wani dan siyasa da aka tsare tere da shi.
Saurari rahoton Hamid Mahmoud:
Dandalin Mu Tattauna