Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwararru Na Ci gaba da Tsokaci kan Nadi Ministoci


Jerin Ministoci
Jerin Ministoci

Tsohon Gwamnan jihar Lagos, Babatunde Raji Fashola, aka durawa alhakin tafiyarda ma’aikatar ayyuka da gidaje da makamashi

Hade ma’aikatar ayyuka da gidaje da makamashi wurin guda karkashin Minista daya na ci gaba da jan hankalin kwararru a Najeriya.

Tsohon Gwamnan jihar Lagos, Babatunde Raji Fashola, aka durawa alhakin tafiyarda wannan bangare.

Korarrun Inginiyoyi irinsu Manu Ibrahim, na da kwarin gwiwar cewa fashola ka iya cire kitse daga wuta. Yana mai cewa kasancewar Fashola yayi abun tasiri a jihar Lagos ai kaga yanzu an kara fadadamasa.

Ya kara da cewa babban kalubale ne ke gareshi kuma aikin ne da yake bukatar hannu dayawa daga kowane fani.

A daya bangare kuma nadin da aka yiwa dan jarida Adamu Adamu, a matsayin Ministan Ilimi da kuma Farfesa Anthony Onwuka, a matsayin karamin MInista shima masu sharhi na kalon abun ta mahanga daban daban.

Jafar Jafar wani dan jarida dake Abuja ya ce Farfesa Onwuka, kwararren malami mne na makaranta a harkar ilimi shi gangaran ne Adamu Adamu shima kwararre ne a harkar jarida amma gaskiya a tsari na aiki bai dace asa wanda ikai matsayin Farfesa a saman Farfesa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG