Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zan Maida Hankali Sosai Ga Batun Matasa In Ji Solomon Dalong


Solomon Dalong yana gaisawa da shugaba Muhammadu Buhari bayan an rantsar da shi a matsayin ministan matasa da wasanni
Solomon Dalong yana gaisawa da shugaba Muhammadu Buhari bayan an rantsar da shi a matsayin ministan matasa da wasanni

Sabon ministan harkokin matasa da wasanni ya fadawa VOA Hausa cewa zai bayar da hankali sosai ga batun matasa, duk da cewa bai shiga ya ga halin da ma'aikatarsa take ciki ba tukuna.

Sabon ministan harkokin wasanni da matasa na Najeriya, Barrista Solomon Dalung, ya bayyana cewa zai bayar da hankalinsa ga batun kyautata halin da matasan Najeriya ke ciki, duk kuwa da cewa bai shiga ma'aikatar ya ga halin da take ciki ba.

A lokacin da yake tattaunawa da wakilin VOA Hausa, Umar Faruk Musa, Mr. Dalung yace akwai bambanci kan batun yadda za a iya yin gyara ga wanda yake kallo daga waje, da kuma wanda yake kallo daga ciki. Don haka zai fi so sai ya shiga ya ga abubuwan da ake da su a kasa, kafin ya yanke shawarar abinda zai yi.

Minista Dalung ya ce, "tun da yanzu ne aka rantsar da mu, to sai mun shiga gidan (mun) duba, mu san mecece ke kasa, daga nan sai mu san inda za mku tinkara, muyi masa gyara."

Amma dai ya ce "harkar matasa na bukatar a sa hankali (a kai) domin a cece su, kuma a horar da su, su zamo shugabanni na kwarai gobe."

Zamu Maida Hankali Ga Matasa In Ji Solomon Dalong - 1'00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG