Babban hafsan sojojin Najeriya Laftanar Kanar Tukur Baratai , shine ya yi alkawarin kafa wannan kwamiti domin tabbatar da da’a tsakanin sojojin Najeriya. Babban hafsan yace babu shakka an zargi wadansu sojoji da shiga harkokin siyasa dumu dumu, yace idan bincike ya tabbatar da wadansu jami’an sojan suna da laifi, za a ladabtar da su bisa ga abinda doka ta shinfida.
Yace rundunar sojin Najeriya ba zata lamunci rashin da’a ba, kuma tilas ne sojoji su nisanci harkokin siyasa.
Wannan kwamitin da babban hafsan sojojin Najeriyan ya kafa, na karkashin jagorancin majo janar Adeniyi Oyebade, babban hafsa dake rundunar soji ta daya dake Kaduna, yayinda kanar Abdullahi Salihu zai kasance sakatare.
Sanarwar da rundunar sojan ta aikawa manema labarai, ta bukaci dukan ‘yan Najeriya dake da korafe korafe, game da rawar da sojoji suka taka a zabukan da suka gabata a kasar, da su aike da kokensu ko kuma shaidu ga kwamitin da zai yi zama a rundunar soji ta daya dake Kaduna.
Ga cikakken rahoton da wakilinmu a birnin Ikko Babangida Jibril ya aiko.