Shugaban kungiyar Interfaith Mediation Center ta jihar Filato a bangaren addinin Kirista, Evangelist Joshu’a Ringsum yace jihar Filato ta sha fama da tashin hankali a baya, don haka suke jan hankalin bangaren shari’a da ya guji zama sanadin haddasa rudani da tashin hankali a jihar.
Shi ma shugaban kungiyar a bangaren addinin musulunci, Imam Othman Abdullahi Ibrahim, yace sun yi aiki tukuru don ganin al’ummar jihar Filato sun fahinci juna, a saboda haka suke gudun duk wani abu da zai maida hannun agogo baya.
Barista Isyaku Barau, na Sudan Chambers a birnin Kontagora da ke jihar Neja, yace akwai matsala a harkar shari’a a Najeriya da ke bukatar gyara.
Yayin da kotun daukaka karar zabe ta bukaci a sake gudanar da zabuka na wasu ‘yan majalisun tarayya a Filato ta Arewa, a bangare guda kuwa ta umurci hukumar zabe ta kasa da ta kwace takardar shaidar cin zabe ta dan majalisar wakilai daga kudancin jihar Filato, Isaac Kwallu na jam’iyyar PDP, ta bai wa John Dafan na jam’iyyar APC.
Saurari rahoton Zainab Babaji:
Dandalin Mu Tattauna