A ranar Alhamis Kotun kolin Najeriya za ta yanke hukunci kan amincewa da nasarar da shugaba Bola Tinubu ya samu a zaben da ake ta ce-ce-ku-ce a kai ko a’a, kamar yadda wata sanarwar kotu ta nuna a ranar Laraba, bayan da wasu manyan ‘yan takara biyu daga jam’iyyun adawa suka kalubalanci hukuncin da wata karamar kotu ta yanke a watan jiya.
Atiku Abubakar na jam’iyyar People’s Democratic Party da ya zo na biyu, da Peter Obi na jam’iyyar Labour da ya zo na uku a zaben watan Fabrairu, sun yi zargin cewa zaben yana cike da kura-kurai.
Kotun koli ita ce kotu mafi girma a kasar da ta fi yawan al'umma a Afirka, kuma hukuncin da za ta yanke zai zama na karshe.
Ba a tabu samun nasara ba a shari'ar kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya, wacce ta koma kan turbar dimokradiyya a shekarar 1999 bayan kusan shekaru talatin tana mulkin soja a jere, kuma tana da tarihin yawan samun kura-kurai a zabe.
Abubakar da Obi a ranar Litinin din da ta gabata sun bukaci Kotun kolin ta soke hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke a ranar 6 ga watan Satumba, inda ta tabbatar da nasarar Tinubu, a wani yunkuri na karshe na soke sakamakon da kasashen duniya suka amince da shi.
Kotun Kolin tana da kwanaki 60 ta yanke hukuncin.
Lauyoyin Atiku da Obi sun shaida wa Kotun Kolin cewa Kotun sauraren kararrakin zabe ta yi kuskure a lokacin da ta bayyana cewa ba dole bane hukumar zabe ta yi amfani da na’urar tantance sakamakon zabe daga rumfunan zabe, duk da cewa ta yi alkawarin yin hakan.
Sun kuma yi zargin cewa Tinubu bai samu kashi 25% na kuri’un da aka kada a babban birnin tarayya Abuja ba, wanda hakan ke nufin bai cika ka’idar da doka ta tanada ba.
A tsarin dokar zabe a Najeriya, duk dan takarar shugaban kasa da ya samu kasa da kashi daya bisa hudu na kuri'un da aka kada a akalla kashi biyu bisa uku na dukkan jihohi 36 na kasar, har da Abuja, to shi ya lashe zabe.
‘Yan adawa da lauyoyin Tinubu sun yi wa wannan tanadin fassara ta daban.
‘Yan adawar dai sun ce ya kamata wanda ya yi nasara ya samu kashi 25% na kuri’u a kashi uku cikin hudu na jihohin kasar, haka kuma a Abuja, yayin da Tinubu ya musanta cewa kashi 25 cikin 100 na nufin jihohi da kuma Abuja.
~ Reuters
Dandalin Mu Tattauna