Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Koli Ta Yi Fatali Da Karar Atiku Da Obi, Ta Tabbatar Da Tinubu A Matsayin Shugaban Najeriya


Babbar kotun tarayya
Babbar kotun tarayya

Kotun kolin Najeriya mai alkalai 7 karkashin jagorancin mai shari’a John Nyang Okoro, ta yi watsi da kararrakin da Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Leba suka daukaka kan nasarar da Bola Tinubu ya samu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

A ranar Alhamis 26 ga watan Oktobar nan ne kotun kolin Najeriya ta yi watsi da bukatu 7 a kararrakin da ‘yan takarar jam’iyyun adawa na PDP da Leba su suka daukaka a gabanta, suna neman a soke zaben da ya baiwa shugaba Bola Tinubu nasara a zaben watan Febrairu, bisa rashin cancanta, mika takardun bogi, rashin samun kaso 25 a birnin tarayya Abuja, da dai sauransu.

Atiku Abubakar ya nemi kotun da ta ayyana shi a matsayın wanda ya sami nasara a zaben.

Zaman Kotu
Zaman Kotu

Bayan dogon nazari tare da karanta hukuncin kotun da aka fara zamanta tun da misalin karfe 9 na safiyar yau da mai shari’a John Nyang Okoro ya yi, kotun ta yi watsi da bukatun jam’iyyun Leba da PDP a kan cewa sun saba ka’ida, musamman bukatar neman a shigar da sabbin shaidu na tabbatar da cewa shugaba Bola Tinubu ya mikawa hukumar INEC takardun shaidar karatu na bogi a lokacin neman tsayawa takara.

Kenneth Okonkwo lauya kuma daya daga cikin magoya bayan jam’iyyar Leba, ya nuna rashin jin dadin sa ga yadda al’amarin kotun kolin ya kaya, yana mai cewa bai gamsu da matsayar kotun a kan batun shigar da sabbin shaidu ba ganin cewa a bisa dokar da ta kafa kotun ne ake gabatar da shaidu.

Zaman Kotu
Zaman Kotu

Jam’iyyar adawa ta PDP ta bakin sakataren yada labaranta, Debo Ologunagba ta ce tabbatar da shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shekarar 2023 da kotun koli ta yi abin kunya ne kuma hakan ya sanyaya wa ‘yan Najeriya gwiwa a cikin matsin rayuwar da suke ciki

Shugaban jam’iyyar APC da ta sami nasara a kotu, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi marhaban da matakin na kotu inda ya yaba da kokarin jam’iyyun adawa saboda yadda suka yarda da fannin shari’a a cikin tsarin mulkin dimokuradiyyar kasar.

A nasa bangare, masanin kundin tsarin mulkin Najeriya, Barista Mainasara Kogo Umar, ya ce yanzu an kamalla shari’ar zaben watan Febrairu a bisa tanadin doka, kuma ya zamo wajibi a rungumi hukuncin a matsayin sahihi, "shi shugaba Tinubu ya mance da shari’a ya fuskanci shugabancin kasa."

A ranar 6 ga watan Satumban da ya gabata ne kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yi watsi da kararrakin da jam’iyyun Leba da PDP suka shigar na nema soke zaben na watan Febrarun a bisa hujjar cewa an saba ka’ida.

Tun bayan dawowa tsarin mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999 ne ake kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya, daga kan Olu Falae da Obasanjo Har zuwa wannan lokacin tsakanin Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG