Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyi Sun Ce Ba Za Su Zuba Ido Matakan Tsaro Na Sukurkucewa Ba


Shugaba Buhari
Shugaba Buhari

Cibiyar bincike da bunkasa Arewa ta ARDP ta ce ba za ta zuba ido harkokin tsaro na ci gaba da tabarbarewa a cikin kasar ba, saboda alhaki ne da ya rataya a wuyan duk wani dan kasa ya tabbatar da ganin sha’anin tsaro ya inganta a fadin Najeriya.

Shugaban Cibiyar Dakta Usman Bugaje, wanda ke amsa tambayoyin manema labaru a lokacin wani taron manema labaran a birnin Kaduna, ya ce yanzu haka kungiyar ta kammala shirya wani babban taro kan tsarkake tsamin tsaro a Kaduna a watan gobe ta Yuli.

Da yake ci gaba da bayani, Dakta Bugaje ya ce kungiyar ci gaban Arewa ta ARDP tayi hadin gwiwa da kungiyoyi kamar su kungiyar SABMF da SCDDD wurin gudanar da taro a kan gudunmuwar da kowa zai bayar domin shawo kan matsalolin tsaro a kasar.

Dakta Bugaje ya ce dole ne a fada wa gwamnati gaskiya kuma a nuna mata inda ta gaza domin ta gyara aikinta na tsaron al’umma, amma ba wai a yi ta yabon gwamnati alhalin kuma tana nuna gazawarta a kan babban aikinta na kula da sha’anin tsaron kasa.

Ya Kara da cewa suna kokarin duban inda gwamnatin ta gaza ne domin su ma su bada tasu gudunmuwa a matsayin sun a ‘yan kasa domin a gudu tare kuma a tsira tare.

Kungiyar ta ARDP ta ce ta gayyaci duk wasu masu ruwa da tsaki a fannin kula da sha’anin tsaron Najeriya da duk rundunonin tsaro a Najerira, kana ta ce ta tabbatar da sakwannin gayyatar sun isa ga duk wadanda aka bukaci halartarsu.

Ga dai rahoton da Isa Lawal Ikara ya aiko mana daga Kaduna:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG