Matakin haramta tsarin karatun almajirci, na daya daga cikin batutuwan da gwamnatin Najeriya take duba yiwuwar dauka, amma ba abu ne da za a yi shi nan take ba, kamar yadda wasu kafafen yada labarai ke ruwaitowa, inji Garba Shehu, daya daga cikin masu magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari.
Shehu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya aikewa manema labarai da sa hannunsa a karshen makon nan, wacce Muryar Amurka ta samu.
“Duk da cewa gwamnatin Buhari ta dukufa wajen samar da tsarin karatu na kyauta na kuma dole ga kowanne yaro, domin shawo kan matsalar yara da suke fita daga makarantu, matakin haramta karatun alamjaranci zai bi ka’idojin ne da shari’a ta shimfida,” sanarawar ta bayyana.
“Lallai, gwamnatin tarayya tana da burin ganin kowanne yaro da ya kai minzilin zuwa makarantar firaimare yana zuwa makaranta maimakon yawo akan titi yana bara a lokutan zuwa makaranta.”
Sanarwar ta kuma musanta rahotanni da ke cewa za a kama iyayen da ke tura yaransu zuwa makarantu na almajiranci.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne, kamar yadda sanarwar ta nuna, Shugaba Buhari, yayin kaddamar da majalisar kula da tattalin arziki kasa, ya yi kira da a yi taka tsatsan wajen fadin abin da ba daidai ba, dangane da matakin da suke so su dauka kan matsalar almajirai da ke barece-barace.