Rundunar sojojin Najeriya bataliya ta 29, dake runduna ta 6 a birnin Fatakwal tare da wasu jami’an tsaron sa-kai ne suka fafata a wannan farmakin da ‘yan bindiga a yayin da suka yi kokarin satar mai.
Soja daya ya rasa ransa da wasu jami’an sa-kai su 2 sakamakon fito-na-fiton da jami’an tsaron suka yi da ‘yan bindigar. Ba tare da bata lokaci ba sansanonin tsaro daban daban a yankin suka kai agajin gaggawa wurin suka kuma bazama farautar ‘yan bindigar.
Jami’an tsaron sun sami nasarar cafke shugaban kungiyar da aka fi sani da suna Nobel, har aka sami bindigogi daban daban a wurin sa amma shi ma daga bisani ya sheka lahira.
Shugaban runduna ta 6 ta sojin Najeriya, Manjo Janar Jamilu Sharham ya ce rundunarsa zata tabbatar da tsaro a wuraren da ake ayyukan hakar danyen mai a yankin.
Mai fashin baki akan lamuran tsaro, Ahmed Baba Tijjani Gamawa mai ritaya, ya ce kasancewar yanayin tsaro a yankin yanzu, akwai bukatar gwamnati, da gwamnan jihar Rivers, da jami’an tsaro su hau teburin sulhu ba tare da wata akida ta siyasa ba, don a kare rayukan jama’a da dukiyoyin su.
Ga karin bayani a cikin sauti daga Lamido Abubakar Sokoto.
Facebook Forum