Ranar daya ga wannan watan na Mayu ne rundunar 'yan sanda ta Abuja ta turo ASP Kulu Dogonyaro da Elizabeth Oja zuwa Sakkwato domin ci gaba da bincike a kan tuhumar da aka yi musu ta satar yara biyar ciki har da jinjira 'yar makonni kalilan, daga Sakkwato zuwa Abuja.
Tun daga wannan lokacin ne kungiyoyin fafutuka ke kai gwaro sukai mari ganin yadda rundunar zata tafiyar da lamarin musamman ganin ya hada da jami'ar 'yan sanda a ciki, wadda aka ce ta taba aiki a Sakkwato.
Malam Abdulganiyu Abubakar shugaban kungiyar masu fafutuka a kan safarar yara, da sa su aikin wahala na kasa, yace lokacin da lamarin ya faru, kungiyarsu ta jinjina wa 'yan sanda akan kama ma'aikaciyar su da bincike a kanta, kuma duba da cewa batu ne da ya shafi safarar bil'adama, suka yi kira ga rundunar 'yan sanda ta mayar da lamarin ga ofishin hukumar yaki da safarar bil'adama ta kasa.
Ya ce kwana biyu bayan faruwar lamarin a Sakkwato an samu faruwar makamancinsa a jihar Edo tsakanin wata yarinya da mahaifinta ke cin zarafinta, suka kai rahoto ga 'yan sanda kuma aka dauki matakin da ya kamata, sabanin abinda suka samu ga 'yan sanda a Sakkwato.
Hadaddiyar kungiyar kungiyoyin kare hakkin bil'adama ta bakin jami'in bincike da tattara bayanai Ado Abdullahi tace ganin batun na tafiyar hawainiya sai da ta yi zama da kakakin rundunar 'yan sanda ta ji inda aka kwana.
Hakazalika, rundunar 'yan sandar ta bakin kakakin ta ASP Ahmad Ruafa'i ta nuna damuwa akan yadda batun ke fita ta dandalin sada zumunta na yanar gizo, wanda yace barazana ce ga binciken da suke yi, kuma dangane da masu korafi su yi hakuri, zasu san abinda ake ciki idan an kammala bincike.
An jima ana fama da irin wannan matsala a yankunan Najeriya inda ake sato yara daga wani yanki a kai su wani yanki na daban da wasu manufofi na daban.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna