Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ceto Yaran Katsina 30 Da ‘Yan Bidniga Suka Sace Kasa Da Sa'o'i 24 Da Yin Garkuwa Da Su


'Yan sanda Najeriya yayin wani atisaye da suka yi a Abuja (Hoto: Facebook/Rundunar 'Yan sandan Najeriya - Wannan tsohon hoto ne)
'Yan sanda Najeriya yayin wani atisaye da suka yi a Abuja (Hoto: Facebook/Rundunar 'Yan sandan Najeriya - Wannan tsohon hoto ne)

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq, ne ya tabbatar da hakan ga gidan talabijin na Channels a ranar Talata.

Kasa da sa’o’i 24 bayan sace yara 30 a karamar hukumar Batsari a jihar Katsina, rundunar ‘yan sandan jihar ta ce sun sami nasarar kubutar da su.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq, ne ya tabbatar da hakan ga gidan talabijin na Channels a ranar Talata.

Ya kara da cewa sakin nasu ya biyo bayan wani hadin gwiwa da rundunar ta yi da masu ruwa da tsaki, wanda ya yi imanin cewa, an samu sakamako mai kyau.

A ranar Litinin din da ta gabata ne ‘yan bindiga suka yi awon gaba da yaran, galibinsu ‘yan mata, a lokacin da suke diban itace a cikin daji.

“Bayan samun rahoton, rundunar ‘yan sandan ta fara gudanar da bincike don ceto wadanda aka yi garkuwa da su tare da cafke wadanda suka aikata laifin. Nan bada jumawa ba za a sanar wa jama’a karin bayani kan alamarin," in ji ASP Sadiq.

A yau ne takwararsa a jihar Delta ya tabbatar da ceto dalibai tara da aka sace yayin yayin da suke tafiya cikin wata ‘yar karamar motar bas a yankin karamar hukumar Ughelli a ranar Juma’a.

Haka zalika, A baya bayanan ne aka sace dalibai 137 daga wani makarantar firamare a kauyen Kuriga a jihar Kaduna wayanda a makon da ta gabata ne a sako su.

Matsalar satar mutane domin neman kudin fansa ta zama ruwan dare a Najeriya musamman a arewacin kasar, inda ‘yan bindiga kan kaikaici dalibai, mata da yara.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG